in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Libya ta fara fuskantar ainihin kalubale
2011-08-26 13:43:23 cri

Kwanakin baya, dakarun adawa da gwamnatin kasar Libya sun mamaye filin mai launin kore dake cibiyar birnin Tripoli, babban birnin kasar, koda yake har yanzu ba a san ina Mouammer Gaddafi yake ba, amma ko shakka babu, an riga an kammla zamanin Gaddafi wato mulkin Gaddafi, kuma ana iya cewa, wannan shi ne sakamakon tabbas da Gaddafi ya samu a sanadin rashin samun amincewa daga wajen jama'ar kasar Libya a fannonin siyasa da tattalin arziki da kuma aikin soja. Duk da haka, a halin yanzu, babu shugaban kasa a kasar Libya, ban da wannan kuma, ana shakku cewar, ko za a iya mika ikon mulkin kasar cikin lumana, to, duk wadannan alamu sun nuna mana cewa, kasar Libya ta fara fuskantar ainihin kalubalen dake gabanta.

Saboda dakarun adawa da gwamnatin Libya ba su shirya hawa kan kujerar mulkin kasa ba tukuna, amma yanzu, hasashe na nuna an riga an kammala mulkin gwamnatin Gaddafi, kila ne rukunoni daban daban dake cikin dakarun adawa za su yi gwagwarmaya domin neman samun ikon mulkin kasa, wannan shi ne kalubale mafi tsanani da kasar Libya za ta gamu da shi yayin da take gudanar da aikin sake ginawar kasa bayan yakin. Wani babban jami'in kungiyar tsaro ta NATO ya taba karba ziyarar da wata kafar watsa labarai ta yi masa inda ya nuna cewa, dakarun adawa na Libya sun yi nasara kan tashin hankalin da suke ciki, kazalika ita ma kungiyar NATO. Ministan tsaron kasa na kasar Faransa shi ma ya yi kashedin cewa, yanzu Libya tana cikin halin rudani, kuma ba za a iya kawo karshensa cikin gajeren lokaci ba. Daga nan, ana iya cewa, kasashen Turai suna damuwa kan halin da Libya ke ciki.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China