A wannan rana, an gwabza yaki a wasu wurare da ke birnin Tripoli a tsakanin dakaru masu adawa da gwamnatin kasar Libya da sojojin gwamnatin kasar. Dakaru sun kafa wuraren tsinkaya a dukkan mararraban hanyoyi na birnin, don duba motocin dake kai da kawowa. A ran 24 ga wata, shugaban kwamitin wucin gadi na kasar Mustafa Abdul Jallil ya bayyana cewa, yawan mutanen da suka mutu a sakamkon yakin da aka yi a Tripoli ya kai a kalla 400, kuma mutane 2000 sun ji rauni.
A ran 24 ga wata, kakakin dakaru masu adawa da gwamnatin Ahmad Barney ya bayyanawa manema labaru cewa, mai yiyuwa ne Muammer Gaddafi yana zaune a yankin hamada da ke tsakanin yankin kudancin Soult da birnin Sabah. Yanzu, sojojin da ke karkarshin jagorancin Muammer Gaddafi suna ci gaba da mallaka yankin Soult da birnin Sabah.
A wannan rana, shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy ya sanar da cewa, za a shirya wani taro kan halin da kasar Libya take ciki a ran 1 ga wata mai zuwa a birnin Paris, a gun taron za a tattauna kan batun sake gina kasar Libya.(Abubakar)