in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yin watsi da sansanin Bab al-Azizia shi ne wani irin aikin janyewa
2011-08-24 15:52:07 cri

Bayan da sojojin kungiyar adawa ta kasar Libya suka mallaki sansanin Bab al-Azizia dake birnin Tripoli a ran 23 ga wata, shugaban kasar Mouammer al Gaddafi ya yi jawabi a ran 24 ga wata, inda ya ce, yin watsi da sansanin shi ne wani irin aikin janyewa.

A ran 24 ga wata, an gabatar da wannan jawabi a shafin internet na wani gidan telebijin dake karkashin jagorancin dan sa Saif al-Islam Gaddafi. A safiyar 24 ga wata, kakakin shugaba Gaddafi ya bayyana cewa, Gaddafi ya riga ya shirya sosai wajen yaki da kungiyar adawa har na tsawon wasu watanni har ma wasu shekaru a nan gaba.

Yanzu dai sojojin kungiyar adawa ta kasar suna nan suna binciken sansanin. A ran 23 ga wata, kakakin bangaren soja na kungiyar adawa ta kasar Ahmad Bani ya bayyana cewa, kwamitin wucin gadi na kungiyar adawa zai kaurar da cibiyarsa daga birnin Benghazi zuwa birnin Tripoli a kwanaki biyu masu zuwa.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China