in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun adawa da gwamnatin Libya sun mamaye sansanin soja na Bab Al-azizia na Moammar Gaddafi
2011-08-24 13:17:49 cri

A ranar 23 ga wata, dakarun adawa da gwamnatin kasar Libya sun bude wuta ga sansanin soja na Bab Al-azizia na Gaddafi daga Tripoli, babban birnin kasar, a kan mayar da sansanin Azizia a matsayin alamar mulkin Gaddafi, mun samu labara cewa, dakarun adawa sun riga sun mamaye gidan kwanan Gaddafi dake cikin sansanin, amma a halin yanzu, ba a san ina Gaddafi yake sauka ba.

Tun daga ranar 23 ga wata da asuba, dakarun adawa da gwamnatin kasar Libya suka fara kai hari ga sansanin soja na Azizia wanda shi alamar mulkin Gaddafi. Sansanin Azizia yana kudancin Tripoli, fadinsa ya kai kusan kilomita shida, wanda wannan sansanin a nan Gaddafi yake kwana. Dakarun adawa sun yi yini daya suna yin kazamin yaki da sojojin gwamnatin kasar, daga baya, wato a wannan rana da maraice, sun shiga sansanin soja nan kuma suka mamaye gidan kwana na Gaddafi dake cikin sansanin, amma ba su kama Gaddafi a wurin ba. Bisa bidiyon da gidan telibijin na Al Jazeera na kasar Quatar ya bayar, an ce, an rushe wani gini mai hawa biyu dake cikin wannan sansanin soja sosai, kuma an daga tutar kwamitin wucin gadi na duk kasar Libya a gaban wannan gini.

A ranar 23 ga wata da dare, kwamandan dakarun adawa Abdel Bel ya nuna cewa, sun riga sun kammala yakin dake cikin sansanin, kuma sun mamaye wurare kashi 90 cikin dari na sansanin, sojojin gwamnatin kasar Libya a wurare kalilan ne kawai suke iya nuna adawa.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China