A wannan rana, Yang Jiechi ya buga waya ga babban sakataren MDD Ban Ki-moon game da halin da ake ciki a kasar Libya bisa tuntubar sa da aka yi , inda ya bayyana cewa, yanzu dai an shiga muhimmin lokaci a kasar Libya. Kamata ya yi bangarori daban daban na kasar Libyan su kaddamar da aikin siyasa na hadin gwiwa, da samun daidaito don sake gina kasar ta hanyar yin shawarwari cikin lumana.
Kana Yang Jiechi ya jaddada cewa, ya kamata a tabbatar da tsaron hukumomin harkokin waje na kasa da kasa dake kasar Libya tare da ma'aikatansu, yana fatan MDD za ta taka muhimmiyar rawa kan wannan batu.
Ban Ki-moon ya ce, MDD zata taka muhimmiyar rawa wajen taimakawa kasar Libya kan sake ginawa,don haka tana son yin hadin gwiwa tare da kasar Sin kan wannan batu , kuma tana son yin mu'amala tare da hukumomin yankuna da abin ya shafa.(Zainab)