in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar adawa ta kasar Libya ta shiga sansanin Bab al-Azizia
2011-08-24 10:15:43 cri

A ran 23 ga wata da maraice, bayan da aka yi ta bata kashi har na tsawo yini guda, kungiyar adawa ta kasar Libya ta shiga sansanin Bab al-Azizia dake wakiltar ikon shugaban kasar Moammar Gaddafi, kana ta mallaki wurin da Gaddafi ke zaune a sansanin, amma ba a ga Gaddafi ba.

Wani hafsan soja na kungiyar adawa ta kasar Libya ya bayyana cewa, an riga an kawo karshen yakin a sansanin, kungiyarsa ta mallaki kashi 90 cikin kashi dari na sansanin.

A wannan rana, shugaban kungiyar hadin gwiwa ta wasan chess ta duniya Kirsan Nikolayevich Llyumzhinov ya bayyana cewa, Gaddafi ya buga waya gare shi a wannan rana, inda ya ce, yana a birnin Tripoli, kuma ba zai bar kasar Libya ba.

A wannan rana da sassafe a sansanin Bab al-Azizia, dan Gaddafi Saif al-Islam Gaddafi ya bayyana wa 'yan jarida cewa, yanzu dai birnin Tripoli yana karkashin jagorancin shugaba Gaddafi, kana Gaddafi da iyalansa suna nan a birnin .

Bisa labarin da aka bayar, an ce, kungiyar adawa ta kasar Libya ta mallaki birnin Ra's Lanuf, mihimmin birnin dake gabashin kasar, kana ta sa sojojin gwamnatin kasar suka janye zuwa karkarar birnin Bin Jawad. Amma gwamnatin kasar ba ta ce kome akan wannan batu ba.

A halin yanzu dai, an yanke wayar telebijin a kasar, amma ba a yanke na yanar gizo da na sadarwa da kuma wayar tarho ba. Kungiyar adawa ta kasar ta mallaki yawancin yankunan babban birnin kasar da karkararsa, kana tana binciken dukkan mutanen da suke zirga-zirga.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China