in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta ci gaba da inganta hadin gwiwa da kasar Libya a fannin tattalin arziki da cinikayya
2011-08-23 20:41:23 cri

A ranar 23 ga wata, a nan birnin Beijing, mataimakin direkta na sashen kula da harkokin cinikayya da kasashen waje na ma'aikatar harkokin kasuwanci ta Sin Wen Zhongliang ya bayyana cewa, yana fatan yanayin da ake ciki a Libya zai daidaita, kuma Sin za ta ci gaba da inganta hadin gwiwa da kasar Libya a fannin tattalin arziki da cinikayya.

Wen Zhongliang ya fadi haka ne, yayin da ya halarci wani taron manema labaru game da harkokin cinikin da Sin take yi da kasashen waje. Ya ce, saboda sauyin yanayin kasar Libya, akwai tasiri sosai ga yawan jarin da Sin ta zuba a kasar. Haka kuma, ya ce, yawan jarin da Sin ta zuba a kasar, musamman a fannin man fetur, ya nuna hadin gwiwar tattalin arziki ta moriyar juna da ke tsakanin kasashen Sin da Libya, kuma irin wannan hadin gwiwa na da ma'ana sosai ga jama'ar kasar Sin da ta Libya.

Haka kuma, Wen Zhongliang ya bayyana cewa, manufar diplomasiyya da Sin take bi ita ce girmama al'ummomin duniya wajen zabar tsarin siyasarsu, kuma kasar Sin za ta girmama zabin jama'ar kasar Libya.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China