in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ina makomar kasar Libya?
2011-08-23 13:37:53 cri

Bayan da sojojin gwamnatin kasar Libya da dakarun adawa da gwamnatin kasar suka yi rabuwar shekara suna yin gwabzawa da juna, halin siyasa da kasar Libya ke ciki ya yi sauyawa mai ba da mamaki kwanakin baya, dakarun adawa da gwamnatin kasar Libya sun mamaye yawancin unguwoyin birnin Tripoli, babban birnin kasar cikin kwanaki biyu ba tare da gamuwa da wata kiyayya mai karfi ba.

Masu lura da al'amuran yau da kullum suna ganin cewa, dalilan da suka sa dakarun adawa da gwamnatin kasar Libya suka mamaye babban birnin kasar cikin sauri sun kunshi fannoni hudu.

Na farko, a hakika dai, an gano cewa wato tsaron aikin soja na sojojin gwamnatin kasar Libya a Tripoli ba shi da karfi kamar yadda aka kimmanta. Kafin wannan lokaci kuma, wasu masu yin bincike kan aikin soja sun dauka cewa, idan dakarun adawa da gwamnatin kasar sun kai hari ga Tripoli, sojojin gwamnatin kasar wato sojojin Gaddafi za su yi yaki da su har sai sun mutu, ban da wannan kuma, kila ne za su yi amfani da wasu manyan makamai, misali makamai masu linzami da dai sauransu, amma hakikanin gaskiya wannan bai faru ba.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China