Mataimakin shugaban kwamitin wucin gadi na kasar Libya Abdel Hafis Ghoga ya furta a gidan talibijin Al-jazeera da asubahin ranar 22 ga wata cewa, Moammar Gaddafi ya taba zama tauraro a kasar Libya, amma yanzu, jama'ar kasar sun riga sun hambarar da mulkinsa, kasar Libya ta shiga wani sabon zamani.
Abdel Hafis Ghoga ya ce, za a yi babban zabe bisa tsarin mulkin kasar na wucin gadi, yana fatan za a kafa wata kasa ta dimokuradiyya na fararen hula, wannan shi ne burin jama'ar kasar Libya.
Wani wakilin kwamitin wucin gadi na kasar Libya ya bayyana a ran 22 ga wata cewa, jam'iyyar adawa ta riga ta mamaye birnin Tripoli, babban birnin kasar Libya, inda take neman Gaddafi ruwa a jallo, kuma tana kokarin murkushe dakarun sa.