in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sichuan ta kara kyan gani sakamakon farfado da ita daga mummunar girgizar kasa
2011-06-17 17:00:10 cri
Masu karatu, kun tuna da cewa, a ran 12 ga watan Mayu na shekarar 2008, an yi mummunar girgizar kasa mai karfi 8 a ma'aunin Richter a lardin Sichuan da ke kudu maso yammacin kasar Sin, wanda ya yi yalwa da kyan gani, lamarin da ya haifar da mutuwar mutane kimanin dubu 87, yayin da aka yi asarar kudin Sin RMB yuan biliyan 46.6 ta fuskar yawon shakatawa kai tsaye. Bayan shekaru 3, an farfado da lardin na Sichuan. Sakamakon ayyukan farfadowa ta hanyar kimiyya, Sichuan ta sake bayyanawa a gaban mutane, ta kuma kara kyan gani.

Kwanan baya, an bude bikin kasa da kasa na harkokin yawon shakatawa da al'adu a garin Shuimo na gundumar Wenchuan da ke yankin Aba na kabilun Tibet da Qiang mai cin gashin kansa a lardin Sichuan, wanda aka mayar da shi a matsayin abun misali mafi kyau a fannin samun farfadowa bayan bala'i a duk duniya baki daya. A yayin bikin budewar, Zoltan Somogyi, darektan gudanarwa na hukumar yawon shakatawa ta kasa da kasa ya bayyana cewa,"Muhimmin dalilin da ya sa Sichuan ta yi fice a fannin yawon shakatawa shi ne ta yi yalwar wuraren tarihi ta fuskar muhallin halittu da al'adu, musamman ma wuraren yawon shakatawa da aka zabe su a matsayin wuraren tarihi na muhallin halittu na duniya, da tsoffin garuruwa da aka adana su da kyau, da kuma wuraren tarihi da suka taka muhimmiyar rawa ta fuskar al'adu. Ba shakka wadannan fitattun albarkatun yawon shakatwa suna janyo matafiya daga sassa daban daban na gida da wajen kasar Sin zuwa nan Sichuan. Sa'an nan kuma, sun sanya Sichuan za ta iya zama wurin yawon shakatawa da ake Allah-Allah wajen ziyace shi a duniya."

Kuma a madadin hukumar yawon shakatawa ta duniya, Mr. Somogyi ya taya wa Sichuan murnar samun kyawawan sakamako ta fuskar rage radadin bala'i da farfado da kanta bayan bala'in. Yana mai cewar,"Wani muhimmin nufinmu na halartar bikin shi ne kokarin nuna goyon baya da taimakawa mahukuntan Sichuan da jama'arta da suka sha wahalar mummunan bala'in a shekarar 2008, sa'an nan kuma, muna son taya wa gwamnatin Sin murnar samun nasarar rage radadin bala'in da farfado da Sichuan. Yanzu Sichuan ta kara kyan gani."

Garin Shuimo da aka shirya bikin, wani kyakkyawan wuri ne da ke gabar kogin Shouxi, wanda shi ne wani reshen kogin Min. Kafin bala'in, sakamakon dogara da raya masana'antu kwarai da gaske, garin ya yi ta tinkarar matsalar yin amfani da makamashi da yawa da gurbata muhalli matuka. Amma a sanadiyyar sake gina shi bayan bala'in, muhallin halittu ya kyautata matuka a wajen, tare da samun saurin bunkasuwar aikin yawon shakatawa. A cikin jawabinsa a yayin bikin budewar, Shao Qiwei, shugaban hukumar harkokin yawon shakatawa ta kasar Sin ya yi nuni da cewa,"Shirya bikin a nan garin Shuimo, da baje kolin muhimman sakamakon da aka samu a fannin farfado da Sichuan bayan bala'in, alamu ne da ke bayyana cewa, Sichuan ta samu muhimmiyar nasara a fannin farfado da aikin yawon shakatawa a wuraren da bala'in ya rutsa da su, Sichuan ta bude sabon shafi wajen raya aikin yawon shakatawa."

A yayin bikin, an gabatar da wasu hanyoyin ziyara bayan bala'in, inda kuma ziyartar yankunan karkara ya fi janyo hankalin matafiya. Ana iya jin dadin yin tattaki a dimbin yankunan karkara masu siga ta musamman. Ko wane kauye ya sha bamban da juna, ko wace gunduma ma haka take, sun bayyana siggogin musamman da kabilun Tibet da Qiang suke da su sosai.

Kauyen Pingtou da ke gundumar Mao a yankin Aba, wani kyakkyawan kauye ne da 'yan kabilar Qiang masu kirki suke zaune. Gine-gine irin na kabilar Qiang da kyan muhallin halittu sun burge matafiya masu tarin yawa. Siggogin musamman na kabilar ta Qiang da kauyen ke da su sun tsayar da kafafun matafiya don su kara sani. A kauyen, mazauna wurin, musamman ma 'yan mata kan yi raye-raye irin na kabilar Qiang wato Salang tare da kide-kiden da ake samarwa ta hanyar amfani da gangar da aka kera da fatan tunkiya da sarewa.

Garin Pingtou shi ne ya samun farfadowa bayan mummunar girgizar kasar. A lokacin da mazauna wurin suke sake gina gidajensu, sun mayar da kiyaye da gadon al'adun kabilar Qiang a muhimmin matsayi, sun kuma kare al'adunsu ta hanyar kimiyya. Chen Taixi, mataimakin shugaban hukumar aiwatar da dokokin fuskar yawon shakatawa ta yankin Aba ya yi bayani da cewa,"Kabilar Qiang, wata tsohuwar kabila ce a nan kasar Sin. Sakamakon wucewar lokaci, an raunana al'adun kabilar ta Qiang, musamman ma a wuraren da ake samun 'yan kabilar, kamar gundumomin Mao da Wenchuan da Beichuan. Ko da yake kafin bala'in girgizar kasar, kasar Sin ta mai da hankali kan kubuta da al'adun kabilar Qiang, amma wannan bai isa ba. Bayan bala'in kuma, duk kabilar Qiang ta jawo hankali sosai. Gwamnatin Sin ta kaddamar da aikin yayyata da nazarin al'adun kabilar Qiang. Yankinmu kuma mun gabatar da wasu al'adun gargajiya ga matafiya, wadanda aka iya karanta cikin littattafai kawai a baya. Haka zalika muna fatan ta hanyar gudanar da irin wannan harka da yi nazari sosai, al'adunmu na kabilar Qiang zai ci gaba da kasancewa a duniya."

Sim Su-Bo, wata 'yar kasar Korea ta Kudu da take ziyara a wurin. A ganinta, sakamakon bunkasuwar kasa a zamanance, kuma matasa sun balaga, an raunana kyan surar wasu al'adun gargajiya sannu a hankali. A lokacin da take kara sanin yadda mahukuntan wurin suke kokarin kiyaye da yayyata al'adun gargajiyar kabilar Qiang, hakan ya girgiza Sim sosai, inda ta ce,

"Al'adun kananan kabilu, fifiko ne mai wuyar samuwa da kasar Sin take da shi. Kiyaye su da kuma raya su yadda ya kamata na taka muhimmiyar rawa. A matsayina na wata 'yar kasar Korea ta Kudu, ina amincewa da yadda ake kiyaye wdannan al'adun kabilu na gargajiya."

A cikin hanyoyin yawon shakatawa da aka gabatar bayan bala'in, akwai wasu wuraren da muka sha ji sunayensu sosai sakamakon abkuwar girgizar kasar a ran 12 ga watan Mayu a shekarar 2008, kamar su gundumar Beichuan da birnin Mianyang da dai sauransu. Yanzu haka sun sake tsayawa a kudu maso yammacin kasar Sin cikin sabuwar sura.

Masu karatu, yanzu haka, sakamakon samun farfadowa daga wajen mummunar bala'in, Sichuan ta kara kyan gani, tana jiran zuwan matafiya daga sassa daband aban na duniya domin kara fahimtar kyan surarta.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China