in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bangarori daban daban suna kokarin bunkasa yankin Tibet
2011-06-05 21:35:56 cri
Ibrahim: Gwamnatin tsakiya ta kasar Sin da tsohuwar gwamnatin yankin Tibet sun kulla "yarjejeniyar 'yantar da yankin Tibet cikin lumana" wadda ta kawo haske ga al'ummomin yankin ta fuskar samun wayewar kai na zamani yau shekaru 60 da suka gabata. A jajibirin ranar cika shekaru 60 da 'yantar da yankin Tibet cikin lumana, wakilan CRI sun kai ziyara wurare daban daban na yankin, inda suka yi hira da fararen hula da masu yawon shakatawa domin kokarin fahimtar irin ci gaban da aka samu a yankin Tibet. Amma wani al'amari mai ban sha'awa shi ne, ko da yake yankin Tibet yana kara kokarin shigar da kwararru yankin, amma kamfanoni da mutane da yawa wadanda suke kokarin samun bunkasa suna fatan za su iya horar da mutane wurin ta yadda za su zama kwararru.

Sanusi: Sakamakon kasancewar wani yanayi na musamman a yankin Tibet, an dade ana fama da rashin 'ya'yan itatuwa da kayayyakin lambu a kasuwar Tibet. Mr. Yu Guoqing da uwargidansa wadanda suka fito daga birnin Beijing 'yan kasuwa ne. Bayan sun samu wannan labari, nan da nan suka je yankin Tibet suka kuma yi bincike a kasuwar yankin, sannan suka kafa wani sansanin sayar da 'ya'yan itatuwa a birnin Lhasa. Lokacin da yake bayani dalilin da ya sa suka kafa wannan sansanin cinikin 'ya'yan itatuwa a yankin Tibet, Yu Guoqing ya gaya wa wakilinmu cewa, "Yankin Tibet ne wuri kadai mai tsabta a yanzu a duniya wajen noman 'ya'yan itatuwa domin ba a gurbata shi ba tukuna. Bugu da kari, ana samun isashen hasken rana, kuma akwai zafi da rana, amma akwai sanyi da dare a yankin Tibet, wannan yanayi yana taimakawa bishiyoyin 'ya'yan itatuwa."

Ibrahim: Amma sabo da wannan sansanin 'ya'yan itatuwa yana yankin Qinghai-Tibet mai tsaunuka, babu ni'imtattun gonaki ga bishiyoyin 'ya'yan itatuwa. Sabo da haka, kafin ya fara noman bishiyoyin 'ya'yan itatuwa da yawa, sai da Yu Guoqing da uwargidansa suka yi gwaje-gwaje sau da yawa, inda suka noma 'ya'yan itatuwa iri iri. Bayan ya samu nasarar wadannan gwaje-gwaje, ya yada wa manoma wurin fasahohin da ya samu. Mr. Yu ya ce, "Bayan na samu nasarar gwaje-gwajen da na yi, na koyarwa manoma fasahar kyauta. Hakan ya sa 'yan uwanmu 'yan kabilar Tibet su ma suka kwaikwaye mu wajen noman bishiyoyin 'ya'yan itatuwa, sannan muka sayi 'ya'yan itatuwa daga hannunsu."

Sanusi: E, malam Ibrahim, wannan hanyar da Yu Guoqing ya yi amfani ita ce, kamfani da sansani da manoma suke hadin gwiwar noma da kuma sayar da kayayyakin aikin gona. Madam Liu Wei, uwargidan Yu Guoqing ta gaya wa wakilinmu cewa, bayan an yi amfani da wannan hanya, manoman kabilar Tibet ba su da wata damuwa wajen sayar da kayansu.

"Mun samar wa manoma iri da fasahohi na noman bishiyoyin 'ya'yan itatuwa kyauta, sannan mun sayi 'ya'yan itatuwa daga hannunsu. Yanzu, manoma da yawa sun damu da cewa, mai yiyuwa ne ba za su iya sayar da kayayyakin amfanin gona kamar yadda suke fata ba. Sabo da haka, muka tsai da niyyar sayen dukkan kayayyakinsu bisa wani farashin da muka tsayar da manoma."

Ibrahim: Yanzu, a cikin sansanin noman bishiyoyin 'ya'yan itatuwa da Mr. Yu Guoqing da uwargidansa suka kafa a Lhasa na yankin Tibet, akwai gidajen samun hasken rana 92, inda ake noman bishiyoyin 'ya'yan itatuwa na Strawberry, kuma yawan 'ya'yan itatuwa na Strawberry da ake samu daga kowane irin wannan gida ya kai kimanin kilo 1500 da darajarsu ta kan kai kimanin kudin Sin yuan dubu 30. Sakamakon haka, ba ma kawai an koyarwa manoman wurin fasahohin noman 'ya'yan itatuwa ba, har ma wadannan manoma suna samun albashi a kowane wata.

Sanusi: A cikin shirinmu na baya, mun bayyana muku yadda Mr. Yu Guoqing da uwargidansa suka bunkasa kasuwar cinikin 'ya'yan itatuwa a yankin Tibet, kuma sun samu nasara sosai. Yanzu ga wani mutum na daban wanda yake tafiyar da wani kamfanin samar da takarda a Lhasa, inda aka zuba kudin Sin yuan miliyan 250 kan wani shirin sake yin amfani da takardun da aka yi amfani da su domin samar da wata sabuwar takarda. Mr. Wang Long wanda ya fito daga lardin Shan'xi, kuma ya kware wajen yin takarda ya je yankin Tibet bisa gayyatar da aka yi masa, kuma ya zama mataimakin babban direktan wannan kamfani. A da, kai ziyara yankin Tibet shi ne fata kawai da yake kasancewa a cikin zuciyarsa. "A cikin zukatanmu, yankin Tibet wuri ne na al'ajabi mai tsabta kwarai. Sabo da haka, na dade ina son kawo ziyara yankin."

Ibrahim: Amma, malam Sanusi, ka sani, a matsayinsa na kwararre wajen takarda, Mr. Wang Long bai ji dadi ba ga halin da ake ciki a yankin Tibet wajen tara takardun da aka yi amfani da su. Ka ji yadda Wang Long ke magana. "Ba a tara takardun da aka yi amfani da su a yankin Tibet wajen guda, ana jefar da su a ko'ina kai tsaye. Yanzu muna kokarin tattara irin wadannan takardu domin sake sarrafa su ta yadda za su zama sabbin takardu."

Sanusi: Ko da yake, Mr. Wang Long ya kai fiye da shekaru 50 da haihuwa, amma ya iya yin amfani da fasahohin yin takarda da ya koya a yankin Tibet. Sabo da haka, duk da cewa bai fahimci al'adu da zaman rayuwa da kuma yanayin yankin Tibet ba, ya tsai da niyyar zuwa yankin Tibet a watan Mayu na bana. "Mutanen yankin Tibet suna namijin kokarin neman kwararru daga sauran wurare. Suna fatan mu zauna mu kuma yi aiki a nan. Mu ma muna fatan mu yi aiki a nan. A sauran wurare, mutanen da suka mallaki fasahar yin takarda sun yi yawa. Amma idan mun yi aiki a nan yankin Tibet, za a iya ganin darajarmu. Bugu da kari, bayan kamfaninmu ya samu bunkasa, za mu iya horar da wasu mutanen wurin wadanda za su mallaki fasahohin yin takarda, wannan zai yi kyakkyawan tasiri ga yankin Tibet."

Ibrahim: malam Sanusi, ka ga Mr. Wang Long ya zo birnin Lhasa ne a wannan wata na Mayu, yanzu zan ba ka labarin wata mace mai suna Yan Guiying wadda ta fito daga lardin Sichuan. Ta zo yankin Tibet ne yau shekaru 10 da suka gabata, sabo da haka, yanzu tana zaune a Lhasa kamar yadda mazauna 'yan Tibet suke yi. A farkon lokacin isarta a yankin Tibet, ta yi aiki a wani kamfani, amma yau shekaru 8 da suka gabata, ta samu wani aikin yi na daban a wani kantin sayar da tufafin samfurin "Jack & Jones" na Turai da aka bude a birnin Lhasa. Yanzu tana tafiyar da kantuna 3 na sayar da tufafin samfurin "Jack & Jones" a Lhasa. Sabo da ta dade tana zaune a Lhasa, ta san yadda al'adun wuri suke samun sauye-sauye a cikin 'yan shekarun nan.

"Alal misali, a lokacin da aka fara sayar da tufafin samfurin 'Jack & Jones' a Lhasa, yawancin mutane wurin ba su amince da shi ba in ban da matasa wadanda suke sha'awar kayayyakin zamani masu karbuwa a duniya."

Sanusi: Amma yanzu, mutanen Lhasa, musamman matasa da yawa sun soma sha'awar salon tufafin Turawa suka zana. Madam Yan ta kara da cewa, "Kamar sawan samfurin tufafin da suka yi suna sosai, ba a amince da su ba yau shekaru 7 ko 8 da suka gabata, amma yanzu an fara sayensu a kai a kai."

Ibrahim: Yawan tufafin da ake sayarwa a irin wadannan kantuna yana ta karuwa sakamakon bunkasar tattalin arziki da zaman rayuwar yankin Tibet mai cin gashin kanta. Sannan, gudummawar da mutane, kamar Mr. Yu Guoqing, Mr. Wang Long da madam yu Guiying na sauran yankunan kasar Sin suka baya ta zama daya daga cikin dalilan da suke ingiza bunkasa yankin Tibet.

Sanusi: malam Ibrahim, a ran 21 ga wata da safe, an shirya gagarumin bikin murnar cika shekaru 60 da 'yantar da yankin Tibet cikin lumana a filin dake gaban fadar Potala ta birnin Lhasa. Mr. Andre, wani saurayi dan kasar Jamus wanda ya yi kwanaki 4 yana ziyara a yankin Tibet, ya gaya wa wakilinmu cewa, a ganinsa, manyan duwatsu da filaye na yankin dukkansu suna jawo hankalinsa kwarai.

"Bayan isowata a yankin Tibet, abubuwan da na gani sun faranta mini zuciyata sosai. A kasarmu Jamus, babu manyan duwatsu kamar na wannan yanki, wannan abin al'ajabi ne." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China