in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na kokarin daidaita matsalolin dake kasancewa tsakanin batutuwan bunkasa sana'ar yawon bude ido da kiyaye muhalli
2011-05-26 16:06:35 cri
Ibrahim: A kan dauka cewa, sana'ar yawon bude ido sana'a ce da ba ta kawo illa ga muhalli. Amma sakamakon bunkasuwar wannan sana'a, an fuskanci matsalolin gurbata muhalli sosai. A kwanan baya, hukumar UNESCO ta M.D.D. ta shirya wani taro a gundumar Libo ta lardin Guizhou dake kudu maso yammacin kasar Sin kan dangantakar dake tsakanin bil Adam da tsirrai, inda aka tattauna kan sana'ar yawon bude ido da musamman kokarin kiyaye ingancin muhalli, kana aka yi muhawara kan yadda za a bunkasa "sana'ar yawon bude ido maras gurbata muhalli", har ma aka fitar da "Sanarwar Libo" a kokarin bunkasa sana'ar yawon bude ido da kuma kiyaye muhalli tare.

Sanusi: Amma malam Ibrahim, ko ka san dalilin da ya sa ake son tafiyar da shirin "yawon bude ido maras gurbata muhalli" a wuraren da aka kebe don kiyaye tsirrai na kasar Sin? Mr. Wang Ding, babban sakataren kwamitin kasar Sin na "shirin kula da dangantakar da ke tsakanin bil Adam da tsirrai" ya bayyana cewa, galibin irin wadannan wurare suna yankuna marasa karfin tattalin arziki ne, kuma akwai mutanen da suke zaune a wurin. Idan an bukaci wadannan mutane su bar garuruwansu, tabbas al'amarin zai kai ga tada hankali. Dalilin da ya sa ake son aiwatar da wannan shirin ke nan wato "daidaita hulda tsakanin bil Adam da tsirrai" ta yadda za a samu hanyar daidaita irin wannan matsala. Mr. Wang Ding ya furta cewa, "Bisa wannan shiri, abin da ya fi muhimmanci shi ne kiyaye ingancin muhallli. Amma a lokacin da ake yin haka, ya kamata a yarda wasu mutane su zauna a wuraren dake dab da irin wadannan unguwanni. Amma dole ne a koyar wa jama'a yadda za su kiyaye muhalli. Alal misali, jama'a suna bukatar itatuwan girki, sabo da haka, muka shigar da wasu fasahohin zamani cikin tsarin , ko samar da kudi ga ayyukan samun iskar gas. Haka kuma, mun shirya wa jama'a wasu kwasa-kwasai domin taimaka musu ta yadda za su tafi da zamani. Sakamakon haka, jama'a ba za su rika sare itatuwa da farautar dabbobi ba, kuma za mu iya cimma burin kiyaye ingancin muhalli."

Ibrahim: e, malam Sanusi, ka sani, aikin kiyaye muhalli da kokarin neman ci gaba sun saba da juna. Sabo da haka, bayan an bullo da tunanin "sana'ar yawon bude ido maras gurbata muhalli", wasu mutane sun dauka cewa, sun samu damar bunkasa sana'ar yawon bude ido. A waje daya kuma, wasu mutane sun dauka cewa, sun samu damar kiyaye muhalli.

Sanusi: Game da wannan matsala, shehun malama Lv Zhi ta jami'ar Peking ta jaddada cewa, "yawon bude ido maras gurbata muhalli" hanya ce da aka zaba domin kokarin kiyaye ingancin muhalli a yayin da ake yawon bude ido. Sakamakon haka, lokacin da ake bunkasa sana'ar yawon bude ido maras gurbata muhalli, ba a shigar da masu yawon bude ido da yawa a irin wadannan wurare ba, idan ba haka ba, ba za a iya tabbatar da ingancin wannan sana'a ba, balle a ba da muhimmanci kan ka'idar kiyaye ingancin muhalli.

Ibrahim: Malam Sanusi, yanzu lokacin da ake kokarin bunkasa yawon bude ido, hanyar kiyaye al'adu iri daban daban ta zama wani batun dake jawo hankalin jama'a sosai. Akwai al'adu iri daban daban a yankunan kananan kabilu da dama na kasar Sin. Bayan da aka bude kofofin wadannan yankuna ga masu yawon bude ido, an shigar da tunani da kayayyaki na sauran wurare a wadannan yankuna, ko shakka babu, za su yi tasiri ga al'adun gargajiya na wadannan kananan kabilu. Amma duk da haka ba a samu wani bambanci a tsakanin wadannan al'adu daban daban ba. Shehun malama Li Wenjun ta jami'ar Peking ta bayyana cewa, "Idan wata kabila ta yi biris da al'adunta, to, tsarin zamantakewarta ma zai bace sannu a hankali. Ba ma kawai muhallin halittu da wannan kabila take yana jawo hankalin masu yawon bude ido ba, har ma ana sha'awar muhallin halittu da al'adunta. Idan har kabilar ba ta da al'adu na musamman, to ke nan babu wani bambanci a tsakanin irin wannan yawon bude ido da sauran yawon shakatawar muhallin halittu. Dole ne kananan kabilu su mai da hankali kan yadda za su nemi ci gaba da kansu da kuma kokarin fahimtar asalinsu."

Sanusi: Amma idan ana son bunkasa irin wannan sana'ar yawon bude ido maras gurbata muhalli, dole ne a ilimantar da jama'a kan wannan batu. Yanzu, a ganin yawancin masu yawon bude ido, yawon bude ido maras gurbata muhalli shi ne kada a zubar da shara a ko'ina, kuma kada a cire furanni da ratsa filayen da aka shuka ciyayi na musamman da dai sauransu. Sabo da haka, yaya za a iya bunkasa sana'ar yawon bude ido maras gurbata muhalli kamar yadda ake fata ya zama wani babban kalubalen dake gaban wadanda suke kokarin bunkasa ta. Saurayi Sun Bin ya dade yana kula da sana'ar hawan duwatsu. Ya bayyana cewa, yanzu wannan sana'a tana kan gaba.

"Har yanzu yawancin mutane ba su san irin wannan yawon shakatawa maras gurbata muhalli ba. Sakamakon haka, mutanen da suke da sha'awar irin wannan yawon shakatawa kadan ne. Amma idan ba su da yawa, to, hukumomin dake tafiyar da wannan sana'a ba za su samu wata riba ba, balle su yayata abubuwan da suke da nasaba da yawon bude ido maras gurbata muhalli. Amma ba za a iya canja irin wannan halin da ake ciki a kwanaki daya ko biyu ba."

Ibrahim: Sai dai Mal. Sanusi akwai bukatar masu yawon bude ido su samu ilmin kiyaye muhalli kafin su je wuraren yawon bude ido, kusan ma in ce dole ne su bi ka'dojin irin wannan yawon bude ido bayan shigarsu wadannan wurare. Wannan yana da muhimmanci sosai. Shehun malama Lv Zhi ta jami'ar Peking tana ganin cewa, "Yawon bude ido maras gurbata muhalli ya kan girgiza zukatan wadanda suka halarci irin wannan yawon bude ido, har ma ba za su manta da shi ba har abada, kuma ya kan canja matsayinsu na zaman rayuwa. Alal misali, bayan wasu sun halarci irin wannan yawon bude ido, sun koma gida kana suka yi murabus daga aikin kamfani domin yin aikin kiyaye ingancin muhalli. Sabo da haka, mu kan fadi cewa, irin wannan yawon bude ido tamkar yadda ake koyarwa jama'a ilmin kiyaye muhalli ne. Amma irin wannan yawon bude ido bai dace da yawancin mutane ba."

Sanusi: E, haka ne, malam Ibrahim. Alal misali, Mr. Lai Pengzhi wanda ya fito daga lardin Taiwan ya canja tsarin zaman rayuwarsa bayan ya yi yawon bude ido maras gurbata muhalli. A da ya kan canja mota cikin shekaru uku-uku, amma bayan ya halarci wani bikin kallon tsuntsaye a lokacin da yake da shekaru 40 da haihuwa, ya fahimci nauyin da ke kansa. Sabo da haka, yanzu ya himmatu ka'in da na'in wajen aikin kiyaye muhalli. Mr. Lai Pengzhi ya bayyana cewa, dalilin da ya sa irin wannan yawon bude ido ya burge shi shi ne, ilmin da ya samu daga wajen mai jagora.

"Idan mai jagora bai ilimantar da mu yadda ya kamata ba, ba za mu iya fahimtar hakikanin abubuwan da yawon bude ido maras gurbata muhalli ya kunsa ba. Kuma ba za mu san muhimmancin gundummomin kare halittu ba. Mai jagora ya kasance tamkar wani abun dake hada mutane da halittu da al'adu."

Ibrahim: Wannan batu haka ya ke Mal. Sanusi, game da batun yawon bude ido maras gurbata muhalli, kasar Sin ta fitar da "Sanarwar Libo", inda ta sanar da cewa, za ta bada muhimmanci kan aikin kiyaye muhalli, kuma za ta kara girmama da kuma kiyaye al'adu daban daban da ake da su. Haka kuma, za ta kara koyar da jama'a ilmin kiyaye muhalli. Bugu da kari, za ta sa kaimi ga jama'a da su halarci ayyukan kiyaye muhalli domin kiyaye moriyarsu. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China