A wannan rana, kungiyar NATO ta sake kai hare-hare ta sama kan birnin Tripoli. Wani rahoto daga gidan telebijin na kasar Libya ya ce, jiragen saman yaki na NATO sun jefa boma-bomai kan benaye biyu na gwamnatin kasar, wadanda ke dab da wurin da Moammar Gaddafi ke zaune na barikin soja na Bab al-Azizia. Kakakin gwamnatin kasar Libya Moussa Ibrahim ya ce, a daya daga cikin benayen biyu da aka kai hare-haren, an ajiye wasu takardun bayanan cin hanci da rashawa da suka shafi wasu tsoffin jami'an gwamnati wadanda suka sauya sheka zuwa bangaren 'yan hamayyar kasar. Moussa Ibrahim ya ce, kungiyar tsaro ta NATO ta kai hare-hare ta sama ne da nufin lalata wadannan takardu.