in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin da sauran kasashen duniya na moriyar juna bayan shigar kasar cikin WTO
2011-04-25 19:38:47 cri

Garba: Bana shekara ce ta cika shekaru 10 da shigar kasar Sin cikin kungiyar cinikayya ta kasa da kasa, wato WTO. Shigar kasar Sin cikin kungiyar WTO muhimmin mataki ne matuka ga ayyukan bude kofa da yin gyare-gyaren tattalin arzikin kasar Sin. A cikin wadannan shekaru 10 da suka gabata, tattalin arzikin kasar ya samu bunkasa, kuma sauran kasashen duniya ma suna morewa damar samun bunkasuwa sakamakon ci gaban da kasar Sin ta samu. Sakamakon haka, Shigar kasar Sin cikin kungiyar WTO ya zama al'amarin tabbatar da moriyar juna mafi ma'ana sosai a tarihin kungiyar.

Sanusi: E, malam Garba, ka sani, a watan Disamba na shekara ta 2001, an shigar da kasar Sin cikin kungiyar WTO bayan da aka yi shawarwari har na tsawon shekaru 15. Mr. Long Yongtu, wakilin farko na shawarwari kan batun shigar kasar Sin cikin kungiyar, kuma tsohon mataimakin ministan kula da harkokin cinikin waje na kasar Sin ya gaya wa wakilinmu cewa, "Kasar Sin ta zama mambar kungiyar WTO ba ma kawai ta shiga wata kungiyar kasa da kasa ba, har ma tana fatan a sa kaimi kan ayyukan yin gyare-gyare a cikin gida da kuma bude kofarta ga sauran kasashen duniya lokacin da take kokarin shiga kungiyar. Sabo da lokacin da ake yin shawarwari kan batun shigar kasarmu cikin kungiyar WTO, ana kuma kokarin ilmantar da mu kan yadda za a bude kofar kasarmu ga sauran kasashen duniya, da kuma bunkasa masana'antu. Yanzu mun gane cewa, matakin bude kofa ga sauran kasashen duniya yana kawo mana kyakkyawan tasiri. Tabbas ne yunkurin bunkasa tattalin arzikin duniya don zama na bai daya ya dore gare mu."

Garba: Amma, shiga cikin kungiyar WTO wani mawuyacin zabi ne na jaruntaka da kasar Sin ta yi a kan ta. Saboda bayan ta shiga kungiyar, dole ne ta karbi ka'idojin kasuwanci da sauran kasashen duniya suka saba da su, kuma dole ne ta dauki matakai na a zo a gani a kokarin cika alkawuran da ta yi ta fuskokin masana'antu da aikin gona da sana'o'in ba da hidima da ikon mallakar fasaha da dai makamatansu. Sabo da haka, lokacin da ake kokarin yin shawarwari kan batun shigar kasar Sin cikin kungiyar WTO, an bayyana mabambanta ra'ayoyi a kasar. Wasu kananan masana'antu sun nuna damuwa matuka. Mr. Long Yongtu ya ce, tabbas ne akwai tasiri mai illa ga wasu mutane da wasu masana'antu sakamakon shigowar masana'antu da albarkatan kasa da kwararru cikin kasar daga kasashen waje. Idan ba a samu cece-ku-ce ba, abin mamaki ne.

Sanusi: Malam Garba, Mr. Pascal Lamy, wato babban direkta na yanzu na kungiyar WTO, kuma tsohon wakilin kasuwanci na kungiyar tarayyar Turai ne, wato EU, kuma ya taba yin shawarwari tare da kasar Sin a madadin kungiyar EU kan batun shigar kasar Sin cikin kungiyar WTO, sakamakon haka, ya san kasar Sin sosai. A yayin taron dandalin tattaunawa na Davos da aka yi a farkon bana, Mr. Lamy ya ce, an samu tasiri sosai ga kasar Sin a fannonin dokoki da tattalin arziki da zamantakewar al'ummomin kasar Sin da dai makamatansu sakamakon shigarta cikin kungiyar WTO. Bugu da kari, kungiyar WTO ta kafa sharuda iri iri ga kasar Sin. Sakamakon haka, kasar Sin ta yi namijin kokari matuka wajen shiga cikin kungiyar. Mene ne kasar Sin ta biya domin shigarta cikin kungiyar WTO? Mr. Chen Deming, ministan kasuwancin kasar Sin na yanzu ya ce, kasar Sin ta sayi wani tikiti mai tsada matuka domin shiga cikin kungiyar WTO, kuma ta gamu da kalubaloli iri iri, yanzu ta zama wata abokiyar cinikayya da take zaune daidai wa daida da sauran mambobin kungiyar.

"A cikin shekaru 10 da suka gabata, matsakaicin yawan harajin kwastam da ake biya ga kasar Sin ya ragu daga kashi 15.3 cikin kashi dari zuwa kashi 9.8 cikin dari. Sannan mun bude kofofin hukumomin ba da hidima da yawansu ya kai 100, haka kuma, mun yi biris da gyara da kuma fitar da dimbin dokokin da yawansu ya kai fiye da dubu 3."

Garba: A farkon lokacin shigar kasar Sin kungiyar WTO, an samu cece ku ce da yawa a cikin gidan kasar Sin. Wasu kasashen waje sun kuma yi shakka kan makomar kasar Sin bayan an shigar da ita cikin kungiyar WTO. Amma yanzu kasar Sin ta ba da amsa kamar yadda ake fata bisa matakan a-zo-a-gani da ta dauka cikin shekaru 10 da suka gabata, wato daya daga cikin lokutan da kasar Sin ta fi samun ci gaba. Yawan kayayyakin da aka fitar daga kasar Sin zuwa kasashen waje ya karu da ninki 4.9, sannan yawan kayayyakin da ake shigowa kasar Sin daga kasashen waje ya karu da ninki 4.7. Haka kuma yawan GDP na kasar Sin ya karu fiye da ninki 2, matsakaicin yawan GDP na kowane mutumin kasar ya karu daga dala dari 8 zuwa dala dubu 4 a shekarar 2010.

Sanusi: Bugu da kari, kamar yadda Mr. Chen Deming, ministan kasuwancin kasar Sin ya fadi, a cikin wadannan shekaru 10 da suka gabata, lokacin da kasar Sin take kokarin hadewa da sauran kasashen duniya, ita da sauran kasashen duniya suna samun moriya da taimakawa juna. Musamman manyan kamfanonin kasa da kasa wadanda suke zuba jari a kasar Sin sun samu riba kai tsaye. Mr. Chen ya ce, "A bara, yawan jarin da kamfanonin kasashen waje suka zuba a nan kasar Sin ya zarce dala biliyan 100, jimillar jarin da suka zuba a kasar cikin shekaru 10 da suka gabata ta kai fiye da dala biliyan 700. Wadannan jarin da suka sa a kasar Sin sun sa masana'antu da yawa sun samu moriya kwarai. Kuma yawan hukumomin nazari da suka kafa a kasar Sin ya kai fiye da 1400. Ribar da suka samu a kasar Sin ta taka rawa sosai wjen tallafawa hedkwatocinsu a kokarin fama da matsalar kudi ta kasa da kasa."

Garba: Dadin dadawa, masana'antun kasar Sin sun hanzarta neman kasuwa a duniya a cikin wadannan shekaru 10 da suka gabata. Mr. Long Yongtu, wato wakilin farko a shawarwari kan batun shigar kasar Sin cikin kungiyar ya ce, "Moriya mafi muhimmanci ga masana'antun kasar Sin ita ce sun samu damar yin takara a kasuwannin kasashen duniya, kuma kayayyakin da suke samarwa na samun karfin yin takara a duniya. Yanzu suna da karfin tinkarar matsaloli iri iri a kasuwannin duniya, kuma suna samun kasuwa sosai a duniya."

Sanusi: Malam Garba, ka sani, yau shekaru 10 da suka gabata, yawan jarin da kasar Sin ta zuba a kasashen waje bai wuce dala biliyan 1 ba, amma ya zuwa shekara ta 2010, yawan jarin da ta zuba a ketare ya kai kusan dala biliyan 60. A bara, kasar Sin ita kanta ta soke harajin kwastam da ta take bugawa kan kasashe 43 wadanda suke fama da kangin talauci. Kuma ba a bukatar biyan harajin kwastam na kayayyakin da nau'o'insu ya kai kashi 95 cikin dari lokacin da ake shigo da su kasar Sin daga wadannan kasashe.

Garba: Bayan shekaru 10 na shigar kasar Sin cikin kungiyar, kasar ta shiga wani sabon matakin bunkasa tattalin arziki, kuma ta zama kasa mafi girma ta biyu wajen shigar da kayayyaki daga kasashen waje. A nan gaba, kasar Sin za ta kara bude kofarta ga kasashen duniya, kuma za ta ci gaba da yin kokarin tsaron ka'idojin da yawancin kasashen duniya suke bi. Mr. Chen Deming ya kara da cewa, kasar Sin za ta kara mai da hankali kan yadda za a iya samun ci gaba tare da samun moriya bai daya tsakanin kasashe daban daban. Mr. Chen ya ce, "Yanzu kasar Sin tana tsara manufofin sa kaimi ga shigowar kayayyaki daga kasashen waje. Muna fatan yawan kudin kayayyakin da za a shigar da su kasar Sin zai ninka sau daya nan da shekaru 5 masu zuwa. Bugu da kari, kasar Sin na kokarin bunkasa kasuwannin cikin gida a kokarin habaka bukatun da ake da su a cikin gida." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China