in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Libiya tana cikin halin kiki-kaka a sakamakon matakan soja da aka dauka cikin wata daya da ya gabata
2011-04-19 17:02:40 cri

Tun daga ran 19 ga watan da ya gabata da kasashen Faransa da Ingila da Amurka suka fara kai farmakin sama ga kasar Libiya zuwa yanzu, wadannan kasashe sun yi wata daya suna daukan matakan soja kan kasar. Amma matakan soja da aka dauka ba su sassauta rikicin kasar Libiya ba. Ya zuwa yanzu, ba a daina yake-yake a tsakanin sojojin Moamer Kadhafi da kungiyar dakaru ba, matsalar jin kai da rikici dake faruwa a kasar ta kara tsananta.

A tsakiyar watan Faburairu na wannan shekara, an yi zanga-zangar nuna kyamar gwamnati a kasar Libiya, lamarin da ya yi sanadiyyar barkewar tarzoma a wasu yankunan kasar. Rikicin da ya barke a tsakanin sojojin gwamnati da kungiyar dakaru ya kara tsananta, wanda kuma ya kawo barazara sosai ga jama'ar kasar. A ran 17 ga watan Maris, kwamitin sulhu na MDD ya zartas da kuduri mai lamba 1973, inda aka yanke shawarar kafa yankin hana zirga-zirgar jiragen sama. Sannan kuma, a ran 19 ga watan Maris, sojojin kasa da kasa dake karkashin jagorancin kasar Amurka sun fara kai farmaki ta sama kan wasu yankunan gwamnatin Kadhafi. Bayan an kwashe wasu kwanaki ana gabza fada yake-yake, sojojin gwamnatin kasar Libiya sunfara fuskantar matsala, baya da haka sun samu hasarar makamai da na'urori da yawa. Bisa taimakon da jiragen saman soja na kasa da kasa suka yi mata, kungiyar dakaru ta cimma nasarar musayar wuta tare da sojojin gwamnatin kasar, inda ta kwace wasu biranen dake gabashin kasar. Ganin yadda wannan yaki zai dauki dogon lokaci, kasashen Amurka da Ingila da kuma sauran kasashe na kokarin matsa kaimi ga kungiyar NATO da ta ci gaba da shugabantar yakin kasar Libiya. A ran 27 ga watan jiyya, kungiyar NATO ta sanar da karbar ikon shugabantar yakin daga wajen kasar Amurka domin cigaba da daukar matakan soja kan kasar Libiya.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China