Sanusi: Sannan Mr. Yang Kaisheng, gwamnan bankin masana'antu da kasuwanci na kasar Sin ya bayyana cewa, "Yanzu bankuna suna bukatar hada kan gwamnatocin matakai daban daban da 'yan kasuwa wadanda suke gina gidaje a kokarin nazarin wata hanyar samar da kudi da ta dace domin tabbatar da samar da gidajen inganta rayuwar jama'a."
Garba: A cikin rahoton da firaminista Wen Jiabao ya yi a madadin gwamnatin kasar Sin a yayin bikin kaddamar da taron shekara-shekara na bana na majaliasar dokokin kasar Sin, ya nuna cewa, a bana, za a gina sabbin gidajen inganta rayuwar jama'a da gyara wasu tsoffin gidaje da yawansu zai kai miliyan 10, sannan za a gyara gidajen da yawansu ya kai miliyan 1 da dubu 500 a yankunan karkara. Bisa shirin da aka tsara, gwamnatin kasar Sin za ta samar da kudin tallafi da yawansa zai kai kudin Sin yuan biliyan 103 ga aikin gina gidajen inganta rayuwar jama'a, sannan za a yi kokarin neman sauran kudin da ake bukata a kasuwa. Amma yaya za a iya samun wannan kudi a kasuwa ya zama wani batun dake jawo hankalin jama'a.
Sanusi: Mr. Qi Ji, mataimakin ministan kula da harkokin gidajen kwana da bunkasa yankunan karkara na kasar Sin ya bayyana cewa, gwamnatin tsakiya da gwamnatocin matakai daban daban za su samar da kudin da yawansa zai kai kudin Sin yuan biliyan 500, sannan hukumomi masu zaman kansu da wadanda suke samun izinin sayen gidajen inganta rayuwar jama'a da kamfanonin da za su samu kwangilolin gina wadannan gidaje ne za su samar da kudin da ake bukata.
Garba: Mr. Ma Mingzhe, shugaban hukumar direktocin kamfanin inshora na Ping'an na kasar Sin ya ba da shawara cewa, ya kamata a yi amfani da kudin inshora domin gina gidajen inganta rayuwar jama'a. Sannan Mr. Yu Lian, babban direktan kamfanin raya birane na kasar Sin ya bayyana ra'ayinsa cewa, "Yaya za a iya warware maganar samun isashen kudin gina gidajen inganta rayuwar jama'a? A ganina, bisa manyan tsare-tsare, ya kamata a yi wannan aiki kamar yadda ake bunkasa masana'antu. Alal misali, yanzu akwai wani kamfanin zirga-zirga na jama'a a kowane birni, me ya sa bu mu kafa wani kamfanin gina gidajen inganta rayuwar jama'a ba?"
Sanusi: Game da wannan batu, Mr. Qi Ji, mataimakin ministan kula da harkokin gidajen kwana da bunkasa yankunan karkara na kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin za ta hanzarta aikin kafa tsarin hada-hadar kudi domin tabbatar da gina gidajen inganta rayuwar jama'a. Mr. Qi ya ce, "Dole ne gwamnatocin matakai daban daban su kebe wasu kasafin kudi ga aikin gina gidajen inganta rayuwar jama'a. Sannan, yanzu muna nazarin yadda hukumomin kudi su nuna goyon bayan wannan aiki, musamman ba da rancen kudi iri na matsakaici da dogon zango ga ayyukan gidajen inganta rayuwar jama'a. Bugu da kari, za mu tsara wasu manufofi ta yadda za a sa kaimi ga kamfanoni da su zuba jari kan ayyukan gina gidaje masu saukin kudi."
Garba: Amma, a ganin wasu kwararru, ba ma kawai dole ne a mai da hankali kan daidaita maganar samu kudi ba, har ma ya kamata a mai da hankali kan yadda za a iya warware batun samar da gidajen inganta rayuwar jama'a gaba daya ba, kuma a kafa dokar dake da nasaba da aikin gina gidajen inganta rayuwar jama'a, wato ya kamata a tsara da kuma aiwatar da manufofin yin amfani da filaye, tabbatar da mutanen da za su iya samun izinin sayen irin wadannan gidaje masu saukin kudi. Bugu da kari, ya kamata a kafa wata hukuma domin tafiyar da wannan aiki musamman.
Sanusi: A cikin shekaru 5 da suka gabata, ba ma kawai gwamnatin kasar Sin ta yi kokarin tabbatar da samar da dimbin gidajen inganta rayuwar jama'a ba, har ma ta yi kokarin kara yawan mutanen da suka samu izinin sayen irin wadannan gidaje masu saukin kudi. Bugu da kari, ban da gidaje masu sauki kudi, ana kuma samar da gidajen haya ga wadanda suke samun kudin shiga kalilan.
Garba: E, haka ne, malam Garba, alal misali, gwamnatin birnin Chongqing ta fi mai da hankali wajen samar da gidajen haya masu arha ga mutane marasa karfi kuma marasa galihu. Game da shirin gina gidajen haya masu saukin kudi, Mr. Huang Qifan, magajin birnin Chongqing ya bayyana cewa, "A shekara ta 2010, yawan gidajen haya masu saukin kudi da muka gina ya kai murabba'in mita miliyan 13. Sannan, mun tsara wani shirin gina gidajen haya masu saukin kudi da yawansu zai kai murabba'in mita miliyan 40 cikin shekaru 3 masu zuwa. Idan wani mutum ya iya samun murabba'in mita 20, to, wadannan gidajen haya masu saukin kudi za su iya biyan bukatun da mazauna miliyan 2 suke da su."
Sanusi: Lokacin da ake tsara shirin gina gidajen inganta rayuwar jama'a, dole ne an fi mai da hankali kan yadda mutane wadanda suka sayi ko suka yi hayar irin wadannan gidaje za su iya samun moriya. A kowane birni, musamman a cikin manyan birane, wadanda suke fama da matsalar wurin kwana, yawan kudin shiga da suke samu ya yi kadan. Idan yawan kudin zirga-zirga ya karu a kowane wata, ko su kan amfani da sa'o'in da yawa kan hanyar zuwa ofis, makaranta, asibiti ko kasuwa, za su nuna damuwa. Saboda haka, lokacin da ake tsara shirin gina gidajen inganta rayuwar jama'a, dole ne a samar da kyakkyawan tsarin zirga-zirgar jama'a da sauran ayyukan yau da kullum, kamar su asibitoci da makarantu da kasuwanni gare su. Hakan zai sa jama'a su ji dadin kwana a cikin irin wadannan gidajen inganta rayuwar jama'a.
Garba: Gwamnatin kasar Sin tana da wani buri, wato tana fatan kowa ya samu kyakkyawan wurin kwana. Saboda haka, a cikin shekaru 5 da suka gabata, ta soma samar da gidajen inganta rayuwar jama'a, sannan a cikin shekaru 5 masu zuwa, za ta samar da karin gidajen inganta rayuwar jama'a, har ma za ta kafa dokar tabbatar da samar wa mutane marara karfi kuma marasa galisu gidajen inganta rayuwar jama'a. (Sanusi Chen)