Sanarwar da ofishin jakadancin kasar Faransa a Cote d'Ivoire ya bayar ta yi nuni da cewa, al'amarin ya faru ne a yayin da sojojin Faransa ke kokarin dauke jakadan kasar Japan a Cote d'Ivoire, a lokacin ne suka fuskanci harbe-harbe daga dakarun Gbagbo. Daga bisani, sojojin Faransa suka mayar da martani da jirgin sama mai saukar ungulu.
Sanarwar ta kara da cewa, bisa ga yadda Japan da MDD suke bukata, sojojin Faransa sun dauke jakadan kasar Japan a Cote d'Ivoire zuwa sansaninsa.