Dakarun jami'an Ouattara sun ce za su dauki matakin soja domin kama Gbagbo da ransa, a kokarin kawo karshen rikicin siyasar da aka shafe watanni da dama ana yi a kasar Cote D'ivoire.
Kakakin jami'an Laurent Gbagbo Mista Ahoua ya fadawa manema labarai cewa, an yi amfani da wasu manyan makamai don kai hare-hare kan fadar Gbagbo. Ahoua ya kuma la'anci dakarun Ouattara da kulla makarkashiyar kashe Gbagbo, haka kuma ya ce rukunin sojojin Faransa dake Cote D'ivoire na Licorne ya samar da tallafin soja ga dakarun Ouattara wajen kai farmaki kan Laurent Gbagbo.
Amma rukunin sojojin Licorne ya musunta wannan zance.(Murtala)