Sanusi: Malam Garba, ka sani, yau fiye da shekaru 30 da suka gabata, lokacin da kasar Sin ta fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, kasar Sin ta bude kasuwa ga kasashen waje ta hanyar amfani da 'yan kwadago da albashi kadan kuma masu tarin yawa a kokarin samun fasahohin zamani daga kasashen waje. Sakamakon haka, manufofin da kasar Sin ta tsara domin kamfanoni masu jarin kasashen waje da masu jarin cikin gida sun bambanta. Alal misali, yawan harajin da kasar Sin take sawa kan kamfanoni masu jarin kasashen waje kadan ne. Game da irin wannan yanayi, Mr. Liu Kegu, mataimakin gwamnan bankin bunkasa kasar Sin yana ganin cewa, irin wadannan manufofi sun zama wajibi a tarihi lokacin da kasar Sin ta fara yin kokarin bunkasa tattalin arziki. Kamar yadda Mr. Liu ya bayyana cewa, "Lokacin da kasashe masu tasowa suka fara bunkasa tattalin arziki, wata matsala mafi tsanani dake gabansu ita ce ba su da isasshen jarin da ake bukata. Saboda haka, jawo jarin kasashen waje da shigar da fasahohin zamani daga kasashe da yankuna masu sukuni sun zama wajibi a tarihi. Kasar Sin tana da wannan tarihi bayan da ta fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje tun daga shekarar 1978."
Garba: Amma, Malam Sanusi, ka ga, yanzu yawan adanannun kudin musaya dake hannun kasar Sin ya kai fiye da dalar Amurka biliyan dubu 2, kuma yawan jarin kasashen waje da aka zuba a kasar Sin a shekarar 2010 kawai ya wuce dalar Amurka biliyan dari 1. Game da halin da ake ciki a kasar Sin ta fuskar yin amfani da jarin kasashen waje, madam Qian Fangli, mataimakiyar direktan hukumar kula da harkokin jarin kasashen waje a ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin tana ganin cewa, "Ya zuwa shekarar 2010, a cikin shekaru 19 da suka gabata a jere kasar Sin tana kan matsayi na farko a duk duniya wajen jawo jarin kasashen waje."
Sanusi: Malam Garba, ko da yake yanzu kasar Sin tana da adanannun kudin musaya da yawa, amma, tana kuma fuskantar matsaloli da yawa, alal misalai, ba ta samu daidaito a tsakanin zuba jari da kashe kudi ba, kuma ba ta da isasshen karfin kirkiro sabbin fasahohin zamani. Tsarin masana'antu bai dace da yadda ake bukata ba. Sakamakon haka, ba za a iya ci gaba da bata lokaci ba wajen sauya salon bunkasa tattalin arzikinta. Saboda haka, kokarin kyautata tsarin sana'o'in da baki 'yan kasuwa suke zuba jari domin inganta masana'antu masu jarin kasashen waje ya zama wata muhimmiyar ka'ida da kasar Sin take bi lokacin da take kokarin jawo jarin kasashen waje yanzu. Game da wannan batu, Mr. Shi Xiangpeng, mataimakin shugaban kwamitin kula da harkokin yankunan Hongkong, Macau da Taiwan na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ya nuna cewa, kasar Sin tana bukatar kirkiro sabuwar hanyar jawo jarin kasashen waje, kuma ya kamata ta daidaita sana'o'in dake jawo jarin kasashen waje. Mr. Shi ya kara da cewa, "Kasar Sin tana da adannanun kudin musaya da yawa. Yanzu tana bukatar shigowa da fasahohin zamani da masana'antu wadanda ba za su gurbata muhalli ba."
Garba: A yayin taron shekara-shekara na majalisar dokokin kasar Sin da aka yi a watan Maris, sauyin yanayin zuba jari a kasar Sin ya zama wani muhimmin batun da ya jawo hankalin 'yan majalisar. A watan Afrilu na bara, kasar Sin ta fitar da "wasu ra'ayoyi kan yadda za a ci gaba da yin amfani da jarin kasashen waje". Wadannan ra'ayoyi suna ba da jagoranci ga aikin yin amfani da jarin kasashen waje yanzu, kuma a nan gaba. Bisa wadannan ra'ayoyi, ana fatan a shigar da jarin kasashen waje ta fuskokin masana'antar da ke samar da na'urorin zamani da masana'antu masu yin amfani da sabbin fasahohin kere-kere da sana'o'in ba da hidima irin na zamani da sabbin makamashi da kuma masana'antun tsimin makamashi da kare muhalli da dai makamatansu.
Sanusi: Bugu da kari, a watan Maris na bana, ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta fitar da kwarya-kwaryan ka'idojin dudduba yadda kamfanoni masu jarin kasashen waje suke sayen kamfanonin kasar Sin. Bisa wadannan ka'idoji, ma'aikatar tana da ikon dakatar da shirye-shiryen saye da sayarwa wadanda za su kawo illa ga kokarin tsaron kasar Sin, ko za su yi tasiri sosai. Sabo da haka, wasu baki 'yan kasuwa sun nuna damuwa kan, ko kasar Sin ta canja manufofinta na bude kofa ga kasashen waje ne? Game da wannan tambaya, Mr. Chen Deming, ministan kasuwancin kasar Sin ya nuna cewa, kasar Sin ba za ta canja manufofin bude kofarta ga kasashen waje ba, ta fitar da wadannan ka'idoji ne a kokarin tsaron kanta lokacin da ake shigowa da jarin kasashen waje. Mr. Chen ya nuna cewa, "Mun soma dudduba yadda kamfanoni masu jarin kasashen waje za su sayi kamfanonin kasar Sin kamar yadda sauran kasashen duniya suka saba yi. Mun yi haka ne domin bayyana niyyarmu ta yin maraba da shigowar jari daga kasashen waje da hannu bibbiyu, kuma lokacin da ake shigowar jari daga kasashen waje, dole ne mu tabbatar da tsaron kasarmu."
Garba: Game da manufofin da kasar Sin ke aiwatarwa ta fuskar jawo jarin kasashen waje, Mr. Wang Jianxi, mataimakin babban direktan kamfanin zuba jari na kasar Sin ya nuna yabo sosai, kuma ya nuna cewa, wannan ya alamta cewa, yanzu mizanin da kasar Sin ke dauka na kusan daidai da wanda sauran kasashen duniya suke dauka, kuma ya alamta cewa, kasar Sin na kokarin kafa wani yanayin zuba jari a bayyane ba tare da wata tangarda ba bisa ma'aunin da aka saba da shi. Mr. Wang Jianxi ya kara da cewa, "Game da manufofin shigo da jarin kasashen waje kasar Sin, yanzu kasar tana kokarin aiwatar da su kamar yadda ake fata. Yanzu baki 'yan kasuwa suna gane irin jarin da kasar Sin ke nunawa maraba, kuma za su iya sanin makomarsu a kasar Sin."
Sanusi: A cikin sabon shiri na shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki da zaman al'ummar kasar Sin da ya bullo a ran 16 ga watan Maris, a cikin shekaru 5 masu zuwa, kasar Sin za ta inganta aikin bude kofa ga kasashen waje da yin amfani da jarin kasashen waje. Game da ka'idojin da za a bi ta fuskar yin amfani da jarin kasashen waje cikin shekaru biyar masu zuwa, Mr. Wen Jiabao, firaministan kasar Sin ya nuna cewa, "Za mu tsaya kan matsayin yin amfani da jarin kasashen waje kamar yadda ake bukata, kuma za mu kara mai da hankali kan yadda za mu shigo da fasahohin zamani da kwararru da sabbin fannonin ilmin zamani. Bugu da kari, muna fatan wasu manyan kamfanoni su kafa cibiyoyinsu na yin nazari a kasar Sin." (Sanusi Chen)