in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Laurent Gbagbo sun nemi dakatar da bude wuta
2011-04-06 14:16:30 cri

Ranar Talata 5 ga wata, Philippe Mangou babban hafsan hafsoshin rundunar tsaron kasar Cote D'ivoire dake nuna biyayya ga Laurent Gbagbo shugaba mai bari gado ya nuna cewa, rundunarsa ta dakatar da yin musayar wuta da sojojin Alassane Ouattara. Kuma ya nemi tawagar MDD dake kasar UNOCI da ta daina bude wuta.

A wannan rana kuma a fadar shugaban kasar Amurka, shugaba Barack Obama ya ba da sanarwa cewa, kamata ya yi Laurent Gbagbo ya mikawa Ouattara mulkin kasar da jingine makamai domin kawo karshen rikicin kasar da kauracewar asarar rayuka.

Dadin dadawa, ministan harkokin waje na kasar Faransa Alain Juppe ya ce, Faransa na da matsayi daya tare da MDD wato bukata Laurent Gbagbo ya sa hannu kan wata yarjejeniyar mikawa Ouattara mulkin kasar.(Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China