Phillippe Mangou ya bayyana niyyar tsagaita bude wuta ne bayan da aka yi ta kai hare-hare kan birnin Abidjan, wato babban birnin kasar Kodivwa ta fuskar tattalin arziki cikin kwanakin da suka gabata. Birnin Abidjan ya kasance sansani na karshe ga Laurent Gbagbo, amma dakaru mabiyan Alassane Ouattara da na kungiyar M.D.D. da kasar Faransa sun yi hadin gwiwa sun kewaye shi a ran 4 ga wata. Hakan ya sa Laurent Gbagbo da mabiyansa sun shiga cikin mawuyacin hali.
A ran 5 ga wata, Mr. Hamadoun Toure, kakakin kungiyar M.D.D. dake kasar Kodivwa ya gaya wa manema labaru ta wayar tarho, cewar a wannan rana, manyan hafsoshi uku na Laurent Gbagbo sun buga waya ga kungiyar M.D.D. dake kasar Kodivwa, inda suka bayyana cewa, sun riga sun ba da umurnin tsagaita bude wuta, kuma suna tsara shirin kawo karshen yaki. Bugu da kari, wadannan manyan hafsoshi suna nuna niyyarsu ta mika makamansu ga kungiyar M.D.D. dake kasar Kodivwa baya da haka kuma sun bukaci kariya daga kungniyar. Mr. Toure ya ce, yanzu Laurent Gbagbo ya rasa mabiya. Haka kuma, a yayin wani taron manema labaru, Mr. Martin Nesirky, kakakin babban sakataren M.D.D. ya sanar da cewa, ana tattaunawa kan batun saukar Laurent Gbagbo daga mukaminsa. Bisa labarin da kungiyar M.D.D. dake kasar Kodivwa ta bayar, an ce, yanzu Laurent Gbagbo a boye yake a wani dakin da boma-bomai ba su ratsa shi dake cikin fadar shugaban kasar Kodivwa, amma dakarun Alassaine Ouattara sun riga sun kewaye shi.
Game da matakin da za a dauka kan Laurent Gbagbo a cikin kwanaki masu zuwa, ya zama wani batun dake jawo hankalin jama'a. A ran 5 ga wata, Mr. Alain Juppe, ministan harkokin wajen kasar Faransa ya ce, Laurent Gbagbo ya samar da sharadinsa na sauka daga iko, amma kasar Faransa da M.D.D. sun neme shi da ya sa hannu kan takardar amincewa da Alassane Ouattara ya lashe zaben shugaban kasar Kodivwa. Bugu da kari, a yayin taron da kwamitin harkokin waje na majalisar dokokin kasar Faransa ya shirya, Mr. Alain Juppe ya bayyana cewa, wani mashawarci na Laurent Gbagbo ya riga ya gana da jakadan kasar Faransa dake kasar Kodivwa domin tattauna kan sharudan saukar Laurent Gbabgo daga mukaminsa da bangarorin da abin ya shafa.
Dadin dadawa, Mr. Ramtane Lamamra, wanda ke shugabancin kwamitin shimfida zaman lafiya da tsaro na kawancen kasashen Afirka, wato AU ya ce, bayan da shugaba na wannan zagaye na kwamitin ya yi shawarwari da Laurent Gbagbo, yana ganin cewa, Laurent Gbagbo ya riga ya fara tunanin yiyuwar sauka daga mukamin shugabancin kasar Kodivwa. Haka kuma, Mr. Ramtane Lamamra ya ce, kungiyar AU ba ta son ganin an kawo wa kasar Kodivwa baraka, kuma ba ta son ganin an ci gaba da yakin basasa a kasar. Kungiyar AU tana fatan a hanzarta kwantar da hankali a kasar Kodivwa, kuma a yi kokarin kafa wani kyakkyawan tushe ga yunkurin shimfida zaman lafiya, dimokuradiyya da sulhu a kasar. (Sanusi Chen)