in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Laurent Gbagbo sun dakatar da bude wuta
2011-04-06 10:16:11 cri

Ranar Talata 5 ga wata, Philippe Mangou babban hafsan hafsoshin rundunar tsaron kasar Cote D'ivoire dake nuna biyayya ga Laurent Gbagbo shugaba mai bari gado ya nuna cewa, rundunarsa ta dakatar da yin musayar wuta da sojojin Alassane Ouattara. Kuma ya nemi tawagar MDD dake kasar UNOCI da ta daina bude wuta.

A wannan rana, Philippe Mangou ya shedawa manema labaru cewa, sojojin bangarori biyu sun dakatar da bude wuta, kuma sun nemi UNOCI ta daina bude wuta domin ganin wasu mihimman wurare sun gamu da hare-haren jiragen sama da sojojin Faransa suka kai a birnin Abidjan.

Ban da wannan kuma, a wannan rana, ofishin daidaita batun jin kai na MDD ya bayyana cewa, sabo da halin da ake ciki a kasar ya kara tsananta, an nuna matukar damuwa ga halin jin kai da ake ciki a Abidjan babban birnin kasar, tallafin jin kai ba zai iya shiga wannan yanki ba.

An labarta cewa, a karshen watan Disamba na shekarar bara, bayan zaben shugaban kasar Cote D'ivoire, Laurent Gbagbo shugaba mai ci a waccan lokaci da firaministan kasar Alassane Ouattara dukkansu sun yi kirari cewa, sun lashe zaben, saboda haka, kasar ta fuskantar halin kaka-nika-yi na kasancewar shugabanni biyu.(Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China