Gaskiya ne, tashe-tashen hankulan da aka samu a gabas ta tsakiya da arewacin kasashen Afrika, da kuma ayyukan sake raya kasar Japan bayan bala'in girgizar kasa za su kara farashin man fetur na duniya, kana za su yi mugun tasiri ga farfadowar tattalin arzikin duniya, musamman ma ga kasashen Turai. Yanzu kasashen Turai na fuskantar yawan basussuka, tun fil azal kasashen dake arewacin Afrika na samar da man fetur ga kasashen Turai. Saboda haka, idan kasashen dake arewacin Afrika ba su iya samar da isashen man fetur ba, to dole ne kasashen Turai su nemi man fetur daga wasu kasashe masu nisa, wannan zai janyo musu kara biyan kudin jigila, wanda zai yi tasiri ga samar da kayayyaki da kuma sayen kayayyaki. Bugu da kari, karuwar farashin man fetur za ta yi babban tasiri ga kasashen da ke dogara kan shigar da man fetur, ciki har da kasar Japan.