in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar UNOCI ta dauki matakin soja da zummar kiyaye fararen hula
2011-04-05 10:10:55 cri

Ranar Litinin 4 ga wata, babban sakataren MDD Ban Ki-Moon ya ba da sanarwa cewa, a wannan rana da yamma misalin karfe 5, tawagar MDD dake kasar Cote D'ivoire UNOCI ta dauki matakin soja kan rundunar sojojin dake karkashin Laurent Gbagbo shugaba mai bari gado, ta aiwatar da wannan mataki ne bisa izinin kwamitin sulhu na MDD da zummar kiyaye kanta da fararen hula.

A cikin sanarwar, Ban Ki-Moon ya nuna matukar damuwa ga halin da Cote D'ivoire ke ciki. Ya ce, a kwanan baya, sojojin dake goyon bayan shugaba Alassane Ouattara ko Lauren Gabagbo sun rika yi musayar wuta har halin da ake ciki ya kara tsananta, wannan ya kasance sakamakon kin mikawa Ouattara mulki da Laurent Gabagbo ya yi. Ban Ki-Moon ya ce, kwanan baya, sojojin Laurent Gabagbo sun yi amfani da manyan makamai kan fararen hula da tawagar UNOCI dake birnin Abidjan, kuma sun kai hari kan rukunin sintiri mai gudanar da ayyukan kiyaye fararen hula da surufin masu raunana, lamarin ya yi sanadiyyar raunukan masu kiyaye zaman lafiya.

Ban Ki-Moon ya nuna cewa, bisa izinin da kuduri mai lamba 1975 da kwamitin sulhu na MDD ke gabatar, ya nemi tawagar da ta dauki matakai yadda ya kamata domin hana amfani da manyan makamai kan fararen hula, kuma bisa izinin da kuduri mai lamba 1962 na kwamitin sulhu na MDD, tawagar ta sami taimako daga sojojin kasar Faransa. Ban da wannan kuma, Ban Ki-Moon ya ce, ya riga ya sanar da kwamitin wannan lamari, mataimakin babban sakataren MDD mai kula da harkokin kiyaye zaman lafiya zai gabatar da gajeren bayyanai kan lamarin.(Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China