in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jama'ar kasashen waje da ke kasar Cote d'ivoire sun fara ficewa daga birnin Abidjan
2011-04-04 21:26:48 cri

Bayan da yanayin tsaro da ake ciki a birnin Abidjan hedkwatar tattalin arziki ta kasar Cote d'ivoire ke ci gaba da tabarbarewa, a ranar 2 ga wata zuwa ranar 3 ga wata da yamma, jama'ar kasashen waje kimanin 167 suka fara ficewa daga birnin Abidjan, kuma akasarinsu sun kasance jama'ar kasashen Faransa da Lebanon ne.

Haka kuma ya zuwa ranar 3 ga wata da safe, jama'ar kasashen waje kimanin 1650 wadanda, rabinsu 'yan kasar Faransa ne, sun tashi zuwa wani sansanin soja Licorne na kasar Faransa da ke kusa da birnin Abidjan.

A ranar 3 ga wata, fadar shugaban kasar Faransa ta ba da sanarwa cewa, domin tabbatar da tsaron Faransawa da ke kasar Cote d'ivoire, kasar ta yanke shawarar tarar jama'arta da ke Cote d'ivoire, kana kuma, za ta tura sojoji kimanin 300 zuwa birnin Abdijan, ta hakan, yawan sojojin kasar Faransa da ke kasar Cote d'ivoire zai karu zuwa 1100.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China