Haka kuma ya zuwa ranar 3 ga wata da safe, jama'ar kasashen waje kimanin 1650 wadanda, rabinsu 'yan kasar Faransa ne, sun tashi zuwa wani sansanin soja Licorne na kasar Faransa da ke kusa da birnin Abidjan.
A ranar 3 ga wata, fadar shugaban kasar Faransa ta ba da sanarwa cewa, domin tabbatar da tsaron Faransawa da ke kasar Cote d'ivoire, kasar ta yanke shawarar tarar jama'arta da ke Cote d'ivoire, kana kuma, za ta tura sojoji kimanin 300 zuwa birnin Abdijan, ta hakan, yawan sojojin kasar Faransa da ke kasar Cote d'ivoire zai karu zuwa 1100.(Bako)