in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na kokarin bunkasa aikin gona lokacin da ake fama da bala'in fari
2011-03-30 20:59:26 cri
Garba: Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, barkanmu da sake saduwa a cikin shirinmu na yau na Tattalin Arzikin kasar Sin. Tun daga watan Oktoba na bara zuwa yanzu, an yi ta fama da bala'in fari a yankunan arewacin kasar Sin inda ake noman alkama. Amma, ta yaya kasar Sin take tabbatar da yin girbin hatsi da kuma kokarin ganin yawan kudin shiga da manoma suke samu ya karu cikin shekaru 7 da suka gabata a jere? Sannan, lokacin da ake fama da bala'in fari mai tsanani a bana, ta yaya gwamnatin kasar Sin take kokarin shawo kan lamarin?

Sanusi: Lardin Helongjiang dake arewa maso gabashin kasar Sin lardi ne mai arzikin filayen gonaki masu albarka. A 'yan shekarun nan, yawan hatsin da a kan fitar daga lardin zuwa sauran sassan kasar Sin kan kai fiye da kilogram biliyan 25 kowace shekara. Sabo da haka, lardin Helongjiang wuri ne mafi girma a kasar Sin wajen fitar da hatsi. A lokacin kakar bara, lokacin da ake girbin hatsi, malam Chang Zhan, manomi ne a lardin ya je wani wurin adana hatsi domin sayar da hatsin da ya samu, inda Chang Zhan ya gaya wa wakilinmu cewa, "Yawan hatsin da na samu ya yi kusan daidai da na bara, wato na samu shinkafa kimanin kilogram dubu 11 da 250 daga eka daya, kuma yawan kudin shiga da na samu ya kai fiye da yuan dubu 40 bayan na sayar da wani kaso na hatsin."

Garba: a shekara ta 2010, jimillar hatsin da kasar Sin ta samu ta kai ton miliyan 540, wato ta karu da kashi 3 cikin kashi dari. Manomi Chang Zhan ma ya yi farin ciki sosai a sanadiyyar girbin hatsi. Lokacin da aka fara noman hatsi a farkon shekara ta 2010, an gamu da bala'in sanyi da na rashin ruwan sama da ba a taba ganin irinsa ba a tarihi a lardin Helongjiang. Kuma ba a lardin Helongjiang kawai ba, an gamu da bala'in fari mai tsanani da ba a taba ganin irinsa ba cikin shekaru fiye dari 1 da suka gabata a larduna 5 dake kudu maso yammacin kasar Sin, inda yawan gonakin da suka gamu da bala'in ya kai fiye da eka miliyan 6. Sannan bayan an shiga lokacin zafi na bara, an gamu da bala'in ambaliyar ruwa a wasu larduna, wadanda muhimman wurare ne da ake noman shinkafa da sauran nau'o'in hatsi. Sakamakon haka, kasar Sin ta gamu da bala'u daga indallahi iri iri wadanda suka kawo illa sosai ga aikin gona a shekara ta 2010.

Sanusi: amma, malam Garba, ka sani, ko da yake an samu bala'u daga indallahi iri iri a lokaci daya a bara, kasar Sin ta ci gaba da yin girbin hatsi cikin shekaru 7 da suka gabata a jere. Sabo da haka, an tabbatar da samar da isashen hatsin da ake bukata a kasuwa, har ma jimillar hatsin da matsakaicin yawan hatsin da kasar Sin ta kan samu daga eka daya dukkansu sun kai wani sabon mataki a tarihi gaba daya. Bugu da kari, matsakaicin yawan kudin shiga da manoma suke samu ya karu cikin sauri a bara. Game da irin wannan kyakkyawan sakamakon da aka samu, Mr. Han Changfu, ministan aikin gona na kasar Sin ya bayyana cewa, "A takaice dai, mun yi nasara ne bisa manufofin da muka aiwatar, da kuma ilmin kimiyya da fasaha da kudin da muka zuba kan aikin gona."

Garba: A cikin shekaru 5 da suka gabata, bi da bi gwamnatin kasar Sin ta fitar da manufofin tallafawa aikin gona da manoma a jere. Alal misali, tun daga shekara ta 2006, kasar Sin ta dakatar da buga haraji kan aikin gona gaba daya. Yawan harajin da aka daukewa manoma ya kai fiye da kudin Sin yuan biliya 130 a kowace shekara sakamakon wannan manufa. Sannan gwamnatin kasar Sin ta kafa tsarin tallafawa manoma. Yawan tallafin kudin da ta bai wa manoma ya kai fiye da kudin Sin yuan biliyan 130 a kowace shekara. Bugu da kari, gwamnatin kasar Sin ta fitar da manufofin tallafawa aikin gona a yankunan arewa maso gabashin kasar, da ma na kudu maso yammacin kasar a kokarin fama da bala'u daga indallahi da suka auku ba zato ba tsammani. Sannan, ta samar da kyautar kudi ga gudumomi 64 wadanda suke fitar da hatsi mai tarin yawa. Wadannan manufofi sun taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga manoma da su yi kokari kan aikin gona.

Sanusi: An dade ana aikin gona bisa yanayin duniya, kuma a sa'i daya ana fama da bala'u daga indallahi, wadanda matsaloli ne mafi tsanani da aka dade ana gamuwa da su a yayin aikin gona na kasar Sin. Amma a cikin 'yan shekarun nan, an soma yin amfani da injunan aikin gona da ilmin kimiyya da fasaha a nan kasar Sin a kokarin kara yawan hatsin da ake samu. A shekarar 2010, yawan mutanen da suka kware kan ilmin aikin gona, kuma su kan je gonaki suna koyar wa manoma ilmin kashe kwari da ilmin ban ruwa da ilmin fama da bala'u daga indallahi da na yin amfani da injunan aikin gona ya kai fiye da dubu 500. Sun bayar da gudummawa sosai wajen samun karuwar yawan hatsi a kasar Sin.

Garba: Mr. Han Changfu, ministan aikin gona na kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin ta shiga lokacin yin amfani da injuna a yayin da take kokarin bunkasa aikin gona. Kamar yadda Mr. Han ya fadi cewa, "A cikin shekaru 5 da suka gabata, yawan gonakin da ake amfani da injuna a kansu ya kai fiye da kashi 52 cikin kashi dari. Yanzu, mu kan ce mun yi girbin hatsi. Wa ya bayar da gudummawa sosai ga karin yawan hatsin da muke samu? Ilmin kimiyya da fasaha ne na aikin gona. Wannan ya alamta cewa, mun soma yin ban kwana da aikin gona na gargajiya, wato yin amfani da mutane da dabbobi, mun soma dogara da injuna lokacin da muke yin akin gona yanzu."

Sanusi: Lallai, malam Garba. Haka kuma, matsakaicin yawan kudin shiga da kowane manomi ya samu a bara ya karu da kudin Sin yuan 766 sakamakon hauhawar farashin kayayyakin abinci, wato ya karu da kashi 11 cikin kashi dari. Shehun malami Zheng Fengtian wanda ke aiki a jami'ar jama'ar kasar Sin ya bayyana cewa, "Yawan albashin da manoma 'yan ci rani suke samu ya karu, kuma farashin gonaki ya karu, sannan farashin kayayyaki iri daban daban ya karu. Idan farashin kayayyakin abinci bai karu ba, ko kadan, yawan kudin shiga da manoma suke samu zai ragu a hakika. Ina tsammanin cewa, farashin kayan abinci ya karu ne sakamakon raguwar darajar kudin Sin na yuan."

Garba: Ko da yake kasar Sin ta yi ta girbin hatsi cikin shekaru da dama a jere, amma har zuwa yanzu kasar Sin na fuskantar matsaloli masu tsanani ta fuskar aikin gona. Alal misali, lokacin da ake fama da bala'in fari a yankunan kudu maso yammacin kasar, kuma ake fama da bala'in ambaliyar ruwa a wasu larduna da dama a bara, wasu matsakaita ko kananan matakan ayyukan ban ruwa ba su wadatar yadda ya kamata ba. Game da wannan matsala, Mr. Chen Xiwen, mataimakin shugaban rukunin jagoranci a aikin yankunan karkara na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya taba bayyana cewa, "Da farko dai an gamu da bala'in fari a farkon shekarar 2010, sannan an gamu da bala'in ambaliyar ruwa a wasu larduna a tsakiyar bara. Dukkanmu mun gane cewa, ba mu da karfin tinkarar bala'i daga indallahi saboda ba mu sa isashen kudi ba wajen samar da isassun ayyukan ban ruwa na yau da kullum masu inganci a cikin shekaru da yawa da suka gabata ba. Idan ba ka da irin wannan karfin tinkarar bala'i daga indallahi, tabbas ne yawan hatsin da kake samu ya ragu."

Sanusi: Game da wannan batu, a gun wani taron manema labaru da ofishin watsa labaru na gwamnatin kasar Sin ya shirya a nan Beijing kwanan baya, Mr. Jiao Yong, mataimakin ministan kula da harkokin makamashin ruwa na kasar Sin ya bayyana cewa, "A cikin takarda ta farko da gwamnatin tsakiya ta bayar a bana, a bayyane take an tabbatar da cewa, za a kara inganta matsakaita da kananan matakan ayyukan ban ruwa wadanda suke da nasaba da aikin gona da wasu kananan koguna, sannan za a samar da karin ayyukan ban ruwa a yankunan kudu maso yammacin kasar a kokarin daidaita matsalar rashin ruwa da ake bukata. Bugu da kari, za a kara zagewa wajen tinkarar bala'in fari cikin gaggawa da kuma daidaita matsalar rashin ruwan sha mai inganci a yankunan karkara."

Garba: Masana sun ce, idan an dauki matakan tallafawa ayyukan ban ruwa, za a iya rage nauyin da aka dora wa manoma, kuma ayyukan ban ruwa za su iya taka rawa sosai wajen sassauta illar da bala'u daga indallahi suke haifarwa manoma. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China