in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Labaru daga jaridun Afirka
2011-03-26 16:22:35 cri
A cikin shirinmu na yau, bari mu fara duba wani labari da muka samu daga jaridar Gaskiya ta fi kwabo ta kasar Nijeriya, wadda aka fita a wannan mako, inda aka bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta Nijeriya ba za ta lamunci tayar da fitina ba a yayin zabe a wannan shekara da muke ciki.

Jaridar Gaskiya ta ce, gwamnatin tarayya ta Nijeriya ta nuna damuwarta a game da yawan rikice-rikecen siyasa a kasar nan, ta kuma ce ba za ta ci gaba da lamuntar wannan hali ba daga kowane jam'iyya ko gungun mutane wanda ka iya haddasa rashin kwanciyar hankali a kasar.

Tuni shugaban kasar, Goodluck Jonathan ya bai wa jami'am tsaro damar zama cikin shiri domin daukar matakin da ta dace na tsayar da tarzoma da ka iya tasowa a lokacin zabe.

Gwamnatin tarayya bayan kammala taronta na mako a ran Laraba ta yi gargadi cewa, doka zai hau kan wanda ya kawo cikas a kan gudanar da zabubbuka ta hanyar tashin hankali da zai sanya rayuwar jama'a cikin hadari.

Da yake bayyana wa manema labarai sakamakon taron majalisar zartarwa ta kasar, ministan yada labarai, Labaran Maku ya ce, gwamnati za ta nuna ba sani ba a kan duk wanda ya tayar da tarzoma don lalata harkar zabubbuka masu zuwa.

Gwamnati a cewar ministan ba ta kaunar tashin hankali, sabo da haka duk wanda ya nemi tashin hankali bai nemi zaman lafiya ba.

Shugaban kasar in ji Labarun Maku ya ce a lokacin taron, 'duk mai neman shugabanci ko yana son a dama da shi a mulkin kasar a kowane mataki, dole ne a bi dokar kasa a kuma mutunta rayuwa da kayayyakin jama'a.'

Goodluck Jonathan ya ci gaba da fada wa taron cewa, 'ya dace a kamfen dinmu mu nuna cewar, a shirye muke mu shugabanci kasarmu domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali. Dimokuradiyya hanya ce ta bin tsari da bin doka yadda ya dace.'

Shi ma da yake karin bayani a kan sakamakon zaben, ministan cikin gida, Mista Emmanuel Ihienacho ya ce gwamnati ta bai wa kowa hakkin gudanar da harkokin siyasa ba tare da nuna bambaci ba, don haka in ji shi duk wanda ya ga cewa, yana da tasa hanyar gudanar harkokin kamfe.

Shi ma da yake nasa bayanin, ministan harkokin 'yan sanda Mista Humphrey Abba ya ce a lokacin ganawarsu da manema labarai, za a tabbatar da cewa, gwamnati za ta yi amfani da doka a kan duk wanda ke neman kawo tashin hankali.

Jama'a masu karatu, bayan haka kuma bari mu sake duba wani labari da muka samu daga jaridar Gaskiya ta fi kwabo ta kasar Nijeriya, wadda aka fita a wannan mako, inda aka mai da hankali sosai kan kasar Libiya, har aka bayyana cewa, shugaban kasar Libiya Gaddafi ya yi jawabin bijirewa.

Jaridar Gaskiya ta fi kwabo ta ce, gidan talabijin na gwamnatin Libiya ya nuna shugaba Mu'ammar Gaddafi yana jawabi ga al'ummar kasar.

Wannan ne dai karo na farko da Kanar Gaddafi ya bayyana a bainar jama'a tun bayan da kasashen yamma da Amurka suka kaddamar da hare-hare a kan kasar ta Libiya ranar Asabar da ta wuce.

A jawabin na bijirewa, wanda ya yi a birnin Tripoli, Kanar Gaddafi ya shaida wa dimbin magoya bayansa cewa, a karshe dai su ne za su yi nasara a kan 'yan tawayen kasar da kuma sojojin kawancen da Amurka, da Faransa, da kuma Birtaniya ke yi wa jagoranci.

A cewarsa al'ummar Libiya kariya ce daga hare-haren da ake kaiwa kasar ta sama.

Kanar Gaddafi ya ce,

'Ga jama'ar a nan, kuma ga Gaddafi a tsakiyar jama'a.'

Ya ci gaba da cewa,

'Wannan ne kariya daga hare-haren ta sama.'

Shugaban Libiya ya kuma ce, wannan wani sabon yaki ne da kasashen yamma suka daura da addinin Musulunci, sa'an nan ya yi kira ga dukkan Musulmi su shiga yaki.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China