A ran 24 ga wata, kasashen yamma sun ci gaba da kai wa kasar Libya hare-hare ta sama, an sake jin amon fashewar boma-bomai a birnin Tripoli, babban birnin kasar Libya da kuma yankunan da ke kewayensa. A ranar kuma, kasar Faransa ta harbi wani jirgin saman yaki na kasar Libya a sararin sama na birnin Misrata da ke da nisan kimanin kilomita 200 daga birnin Tripoli. Greg Bagwell, mataimakin babban kwamandan sojojin sama na kasar Birtaniya ya bayyana kwanan nan cewa, bayan da ake ta kai hare-hare ta sama har na tsawon kwanaki da dama, an riga an raunana karfin sojan kasar Libya a sararin sama. Haka kuma sakamakon kafuwar yankin hana shawagin jiragen sama, kasashen yamma sun fara mai da hankali kan kai wa sojojin kasa na Libya farmaki ta hanyar amfani da jiragen saman yaki, tare da burin raunana sojojin gwamnatin kasar Libya da ke fafatawa da dakaru masu adawa. Kafofin watsa labaru na kasar Amurka sun ba da labari a wannan rana, cewar wannan canji ya sheda cewa, aikin soja da ake gudanar kan kasar Libya ya shiga mataki na biyu.