in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen yamma sun kai hare-hare a Libya domin neman moriya ba wai dalilin jin kai ba.
2011-03-25 16:15:21 cri

Ran 23 ga wata da dare, kasashen Faransa, da Birtaniya, da Amurka, da sauran kasashen yamma sun ci gaba da kai hare-hare daga sama a kasar Libya, wannan ya haddasa mutuwar mutane da dama tare da jikkata. Kasashen yamma sun fara kai hare-hare a kasar Libya ne wai da dalilin hana takurama jama'arkasar a fannin jin kai, amma abin gaskiya shi ne, hare-haren da suka kai wa kasar Libya sun wuce ainihin maganar jin kai sosai. Masharhanta da dama sun nuna cewa, kasashen yamma sun kai hare-hare ne saboda wata akida da neman moriyar tattalin arziki

Mr. Zhang Yongpeng masani kan harkokin kasashen Asiya ta yamma da na Afirka na kasar Sin ya ce, "A ganin kasashen yamma, gwamnatin Gaddafi na wani mulkin na kama karya, a kasar yau da shekaru da dama, gwamnatin Gaddafi ta fara rikici da kasashen yamma kan lamarin hadarin Lockerbie da batun albarkatun man fetur. Ko da yake Gaddafi ya rike matsayinsa, ya zama wani abokan gaba a idon kasashen yamma. Bayan an samu 'juyin juya hali' a wasu kasashen da ke arewancin Afirka, kasashen yamma suna tsammani lokaci hambarad da gwamnatin Gaddafi ya yi."

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China