in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen duniya sun yi kira da warware rikicin Libya ta hanyar yin shawarwari
2011-03-25 16:12:04 cri

A ran 24 ga wata da dare, babban sakataren kungiyar NATO Anders Fogh Rasmussen ya sanar da cewa, kungiyar za ta dauki ikon shugabantar aikin soja a Libya a cikin 'yan kwanaki masu zuwa. A sa'i daya kuma, kasashen duniya sun yi kira da warware rikicin Libya ta hanyar yin shawarwari.

A ran 24 ga wata a hedkwatar MDD dake birnin New York, babban sakataren MDD Ban Ki-Moon ya yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su dauki matakai domin kaucewa mutuwar fararen hula na kasar Libiya

A ran 24 ga wata, ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi ya buga waya ga takwaransa na kasar Jamus Westerwelle, inda ya yi kira ga bangarori daban daban da su daina bude wuta. Kuma ya jaddada cewa, ya kamata a girmama ikon mulki da cikakken yankin kasar Libya, kuma ya kamata a kawo karshen rikici ta hanyar yin shawarwari. Ban da haka kuma, shugaban kwamitin sulhu na wannan wata kuma zaunanen wakilin kasar Sin dake MDD Li Baodong ya bayyana a ran 24 ga wata a gun taron kan batun Libiya da kwamitin sulhu na MDD ya kira cewa, kwamitin sulhu na MDD ya dauki wannan kuduri ne domin kare rayukan jama'ar kasar Libiya, amma ba kashe fararen hula da haddasa rikicin jin kai ba ne.

A ran 24 ga wata, yayin da shugaban kasar Rasha Medvedev ya buga waya zuwa ga shugaban kasar Amurka, ya jaddada cewa, kada matakan soja da wasu kasashe suka dauka su yi sanadiyyar mutuwar fararen hula, kuma dole ne su bi kuduri mai lamba 1973 da kwamitin sulhu na MDD ya dauka.

A wannan rana kuma, shugaban kwamitin kungiyar tarayyar kasashen Afrika (AU) Jean Ping dake ziyara a birnin Paris ya bayyana adawar kungiyar AU kan matakan soja da sauran kasashen duniya suka dauka a kasar Libiya, kana sojojin wadannan kasashe ba su yi musayar ra'ayi sosai da kasashen Afrika kan wannan batu ba.

shugabannin kasashen kungiyar EU sun bayar da sanawa a ran 24 ga wata,  inda suka bayyana cewa, kungiyar tana son warware rikicin Libya ta hanyar siyasa, kuma ya kamata kungiyar tarayyar kasashen Larabawa ta taka muhimmiyar rawa wajen warware rikicin Libya, don aiwatar da kuduri na 1973 da M.D.D ta tsara.

Ban da haka kuma, bisa labarin da gwamnatin kasar Libya ta bayar a ran 24 ga wata, an ce, yawan fararen hula da suka mutu a sakamakon hare-haren da sojojin kasashen Turai da Amurka ya kai kimanin 100.(Abubakar)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China