A ran 23 ga wata, kasar Amurka ta tura jiragen ruwan yaki uku zuwa Bahar Rum don sa hannu cikin aikin soja a kasar Libya. A wannan rana kuma, jiragen ruwan yaki na kungiyar NATO sun fara yin sintiri a bakin tekun da ke kusa da kasar Libya domin aiwatar da kudurin MDD kan hana Libya sufurin makamai. An labarta cewa, kawo yanzu dai kungiyar NATO ta riga ta tattara jiragen ruwan yaki 16 da kasashe shida suka samar, domin gudanar da ayyukan hana Libya sufurin makamai.