in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu kasashen sun yi kira da warware rikicin Libya ta hanyar zaman lafiya
2011-03-24 12:56:03 cri

A ran 23 ga wata da dare, jiragen sama na sojan kasashen Turai sun kai farmaki ga birnin Tripoli, wanda ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula. Kasashen Aljeriya da Ghana da Italy sun yi kira da warware rikicin Libya ta hanyar zaman lafiya.

A ran 25 ga wata, a kasar Habasha, kungiyar AU za ta kira wani taro don tattauna matsalar Libya, wakilan kasashen dindindin na kwamitin sulhu na M.D.D da na kungiyar tarayyar kasashen Larabawa da na kungiyar EU da kasashen Brazil da India za su halarci taron.

A ran 23 ga wata, ministan harkokin waje na kasar Ghana Alhaji Muhammad Mumuni ya bayyana cewa, kasar Ghana tana nuna goyon baya ga jama'ar Libya, kuma tana son kiyaye hakkin jama'ar Libya.(Abubakar)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China