in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen duniya su yi kira da warware rikicin Libya ta hanyar sulhu
2011-03-23 11:49:23 cri

A ran 22 ga wata, kasashen Amurka da Britaniya da Faransa da sauransu sun ci gaba da kai hare-hare da makamai masu linzame kan kasar Libya, ko da yake wasu kasashen duniya sun yi kira da warware rikicin Libya ta hanyar sulhu.

Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Jiang Yu ta bayyana cewa, kasar Sin tana son warware rikicin kasar Libya ta hanyar yin shawarwari. Ya kamata jama'ar kasar Libya su yanke shawarar makomar kasarsu. Kuma kasar Sin tana nuna goyon baya ga kokarin da manzon musamman kan batun Libya na babban sakantaren M.D.D da kungiyar AU da kungiyar tarayyar kasashen Larabawa suke yi ta hanyar dilomasiya.

Shugaban kungiyar AU Jean Ping ya bayyana cewa, kungiyar tana son warware rikicin Libya ta hanyar zaman lafiya, da nuna adawa da amfani da karfin soja ba tare da yin shawarwari ba.

Mataimakin sakantaren kungiyar tarayyar kasashen Larabawa Ahmed Bin Heli ya bayyana cewa, kungiyar tana nuna goyon baya ga kudurin da M.D.D ta tsai da.

Ban da haka kuma kasashen Rasha da Aljeriya da Greece da Turkiya da Korea ta Arewa sun yi kira ga bangarori daban daban da su daina nuna karfin tuwo, da warware rikicin Libya ta hanyar zaman lafiya.(Abubakar)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China