Haka kuma, Madam Jiang Yu ta ce, makasudin kudurin M.D.D shi ne tabbatar da tsaron jama'ar kasar Libya, sabo da haka Sin tana kira ga bangarorin da abin ya shafa da su tsagaita bude wuta nan take, kuma a warware batun kasar Libya cikin lumana. Haka kuma, kasar Sin tana goyon baya ga manzon musamman na sakatare janar na M.D.D da kungiyar AU da kawancen kasashen Larabawa da su yi kokari ta hanyar diplomasiyya don warware wannan batu.
Ban da wannan kuma, sabo da kwamitin sulhu na M.D.D na gudanar da shawarwari kan bukatar kasar Libya ta kira wani taron gaggawa, wasu manema labaru sun tambayi Madam Jiang Yu game da ra'ayin kasar Sin a matsayinta na kasar da ke shugabancin karba-karba na kwamitin sulhu na M.D.D na wannan wata.
A game da haka, Jiang Yu ta bayyana cewa, a matsayinta na shugabar karba-karbar kwamitin sulhu na M.D.D, Sin ta kan sauke nauyin dake kanta cikin adalci, kuma a bayyane. Zuwa yanzu, kwamitin sulhu na M.D.D na ci gaba da yin shawarwari dangane da bukatar kasar Libya, haka kuma bangarori daban daban na kwamitin za su tsaida kuduri game da matakan da za a dauka.(Bako)