in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana kokarin tabbatar da tsaron samar da wutar lantarki bisa makamashin nukiliya
2011-03-21 17:38:38 cri
Jama'a masu karanta, muna fatan kuna cikin koshin lafiya kamar yadda muke a nan birnin Beijing. To, kamar yadda muka saba, da farko za mu karanto wasu wasikun da muka samu daga wajenku. Ga wannan sako daga malam Nuraddeen Ibrahim Adam a Kano, tarayyar Nijeriya, inda ya bayyana cewa, "Na karanta wani labari da ya ja hankali na dangane da karin zuba jarin da kasar Sin ta yi a Afirka don taimakawa wajen wadata nahiyar da hatsi, a shafinku na yanar gizo. Wato abin da ya burge ni, duk da cewa ana fuskantar kalubalen karuwar farashin hatsi, amma kasar Sin na kokarin kara zuba jari a kasashen Afrika don taimaka musu wajen samar da isashen hatsi, kamar dai yadda, Mista Zhang Chunyu, masanin harkokin Asiya ta yamma da Afirka na cibiyar binciken kimiyyar zaman al'umma ta kasar Sin, ya bayyana. Hakika, na yi mamakin jin cewa, daga shekarar 2009 kasar Sin ta fitar da hatsi fiye da ton dubu 550 zuwa kasashen da suke da matsalar karancin hatsi a kasashen Asiya da Afrika, wani abin armashi, har ma da taimakon hatsi na darajar kudin Sin RMB yuan miliyan 263. Abin da ya fi burge ni da wannan labarin, cewa tun daga shekarar 2004 kasar Sin ta horar da jami'an kula da aikin gona dubu 4.2 na kasashen Afrika. Kai lalle, kasar Sin na hidima mai yawa ga kasashen Afirka dake fafutukar samun ci gaba, kuma wannan labari ya nuna halin tausayi da kasar Sin ke da shi kan kasashen Afrika. Kuma ya nuna a fili irin kokarin da kasar Sin ke yi na raya kasashen Afrika ta fannoni da dama da suka hada da na tattalin arziki, ciniki, aikin gona, al'adu, da dai sauransu. Na gode muku sosai da wannan labari, tare da fatan za ku ci gaba da kawo mana makamantan irin wannan labari nan gaba. Sai na ji daga gare ku."

To, mun gode, malam Nuraddeen Ibrahim Adam a Kano, tarayyar Nijeriya. Kamar yadda ka bayyana, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, Sin tana iyakacin kokari domin raya kanta tare da ba da taimako ga kasashen nahiyar Afirka a fannoni daban daban. Dalilin da ya sa haka shi ne bangarorin biyu sun riga sun sada wa juna zumunci cikin dogon lokaci. Bayan haka, kowa ya san cewa, yanzu ana fuskantar karancin abinci a wurare daban daban. Dukkanmu Sinawa muna fatan jama'ar kasashen Afirka za su yi rayuwa lami lafiya, a maimakon fama da matsalar karancin abinci. Da fatan bangarorin biyu za su kara samun moriya tare. Allah ya karfafa dankon zumunci a tsakaninmu, amin.

Sakon malam Nuraddeen Ibrahim Adam ke nan. Bayan haka, malam Salisu Dawanau a Abuja, tarayyar Nijeriya, ya rubuto mana cewa, "Masu iya magana kan ce 'yawan gaisuwa, yafi yawan fada'. A koda yaushe, idan ina cikin nishadi, na kan tuna abokai da aminai, na kan kuma yi musu fatan alheri. Hakika, yau hankalina kwance yake, kuma ina so in isar da gaisuwar sada zumunci gare ku baki daya a sashen Hausa na CRI."

To, mun gode, malam Salisu Dawanau a Abuja, tarayyar Nijeriya. Mun yi farin ciki sosai domin samun sako daga wajenka. Muna fatan za ka ci gaba da kasacewa cikin wannan yanayi mai kyau. Da fatan za ka ci gaba da mai da hankali kan shirye-shiryenmu domin samun nishadi, da aiko mana da wasiku domin bayyana ra'ayoyi da ba da shawarwari masu kyau. Allah ya karfafa dankon zumunci a tsakaninmu, amin.

Sakon malam Salisu Dawanau ke nan. Bayan haka, a kwanan baya, malam Baba Musa a Maiduguri ya aiko da tambayar cewa, "Yanzu kasar Japan tana kokarin daidaita hadarin tashar nukiliya a sakamakon abkuwar bala'in girgizar kasa da igiyar ruwa ta tsunami. Ko wannan yana da hadari sosai? Ko ya yi daidai ne mu ci gaba da amfani da makamashi nukiliya domin samar da wutar lantarki a duniya?" To, yanzu za mu kokarta ba da amsar wannan tambaya, da fatan malam Baba Musa kana sauraronmu.

A sakamakon abkuwar hadarin tashar nukiliya ta Fukushima a Japan, wasu mutane sun fara nuna tababa ga bunkasa da yin amfani da makamashin nukiliya. Ko akwai hadari sosai? Ko tasoshin nukiliya za su hallaka bil'adam baki daya? Tare da wadannan tambayoyi, dan jarida na kamfanin dillancin labaru na Xinhua ya yi hira tare da tsohon babban darektan hukumar IAEA, Hans Blix, wanda ya bayyana cewa, tare da samun bunkasuwar fasahohi, ana iya tabbatar da tsaron samar da wutar lantarki bisa makamashin nukiliya a kai a kai. A nan gaba, za a ci gaba da samun bunkasuwa a wannan fanni, sabo da mutane ba za su rasa shi ba a yanzu.

Hans Blix ya furta cewa, "A sakamakon abkuwar hadarin tashar nukiliya a Japan, an kara samun muryar yaki da bunkasa makamashin nukiliya a kasa da kasa. Amma a cikin shekaru sama da 10 da suka gabata, an samu kyautatuwa a kai a kai."

Game da makomar makamashin nukiliya, Hans Blix yana zaton cewa, a cikin gajeren lokaci mai zuwa, kila hadarin tashar nukiliya ta Fukushima zai kawo illa ga bunkasa makamashin nukiliya wajen samar da wutar lantarki a kasashen duniya. Saurin bunkasuwa zai ragu. Amma a cikin dogon lokaci mai zuwa, dole ne za a kara raya makamashin nukiliya.

Bayan haka, Vladimir Chuprov, babban masani kan tattalin arziki da makamashi na kungiyar kiyaye muhalli ta duniya mai taken "Greenpeace" a Rasha ya nuna cewa, dole ne a yi taka-tsantsan wajen bunkasa da yin amfani da makamashin nukiliya. A cikin wannan yanayi, kasa da kasa za su rika la'akari da neman wasu sauran makamashi da ba su kawo illa domin maye gurbin makamashin nukiliya. Ya ce,

"Kasashe da yawa sun riga sun yi kokari a wannan fanni. Kamar Isra'ila, tana yunkurin samar da wutar lantarki bisa iskar gas. Kuma ta samu albarkatun makamashin hasken rana. Jamus kuma tana kokarin samar da wutar lantarki bisa karfin iska da kuma iskar gas, yayin da Amurka take yin nazari kan samar da wutar lantarki bisa iskar gas."

Babban sakataren kungiyar hadin gwiwa da bunkasa tattalin arziki Angel Gurria ya bayyana cewa, kasa da kasa suna ta mai da hankali kan yin tsimin makamashi da rage fitar da gurbatacciyar iska. Yana fatan hadarin tashar nukiliya ta Fukushima a Japan ba zai kawo babbar illa ga bil'adam ba.

Jama'a masu karanta, bayani ke nan kan tambayar malam Baba Musa, da fatan ka ga ka gamsu da shi. (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China