in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta kafa tsarin sabon layin dogo mai saurin tafiya mafi girma a duniya
2011-03-21 10:47:51 cri

Ibrahim: Jirgin kasa mai saurin tafiya, wani sabon salon sufurin kayayyaki da fasinjoji ne cikin sauri dake iya tsimin makamashi ba tare da gurbata muhalli ba kuma yana jawo hankalin jama'a sosai. Bayan da aka shiga karni na 21, gwamnatin kasar Sin ta tsayar da kudurin shimfida sabbin layukan dogo masu saurin tafiya domin bunkasa tattalin arziki da zamanintar da tsarin layukan dogo. Bisa wannan manufa, a cikin shekaru 10 da suka gabata, wato ya zuwa yanzu, tsawon sabbin layukan dogo masu saurin tafiya da aka shimfida a kasar Sin ya kai kilomita dubu 13.

Sanusi: lallai, malam Ibrahim, ka sani, kasar Sin kasa ce mai girma, kuma mai yawan mutane. Sannan ba a samu daidaito a tsakanin yankuna daban daban na kasar ta fuskar bunkasa tattalin arziki ba. Sakamakon haka, a cikin dogon lokacin da ya wuce, hukumomin zirga-zirgar jiragen kasa su kan fuskanci matsin lamba sosai. Amma kafin shekara ta 2000, kasar Sin ta fuskanci koma baya wajen kafa tsarin zirga-zirgar jiragen kasa idan an kwatanta su da wasu kasashe masu karfin arziki. Sabo da haka, gwamnatin kasar Sin ta fitar da "shirin bunkasa harkokin jiragen kasa cikin matsakaici da dogon lokaci a nan gaba" a watan Janairu na shekara ta 2004. Wannan ne wani babban shiri na farko da kasar Sin ta tsara domin bunkasa harkokin jiragen kasa cikin dogon lokaci a tarihi. Bisa wannan shiri, an tabbatar da cewa, ya zuwa shekarar 2020, jimillar tsawon layukan dogo da za a samar za ta kai kilomita dubu dari 1, kuma daga cikinsu, tsawon layukan dogo masu saurin tafiya da jiragen kasa masu saurin tafiya da za su yi gudu da ya kai fiye da kilomita 200 cikin sa'a daya ya kai kilomita dubu 12. Mr. He Huawu, babban injiniya a ma'aikatar kula da harkokin jirgin kasa ta kasar Sin ya bayyana cewa, a shekara ta 2004, an tabbatar da aikin shimfida sabbin layukan dogo masu saurin tafiya a tsakanin muhimman birane daban daban wanda ya zama muhimmin aiki. Bayan shekaru 4 kawai, an samu nasarar shimfida sabon layin dogo mai saurin tafiya na farko a kasar Sin. Kamar yadda Mr. He ya ce, "Mun tattara dukkan karfinmu wajen samar da muhimman ayyukan yau da kullum. A cikin gajeren lokaci, mun yi nasarar kammala ayyukan haha-hadar kudi da shigo da sabbin fasahohin zamani daga kasashen waje, sannan mun kirkiro fasahohin zamani dake dacewa da hakikanin halin da ake ciki a kasar Sin. Haka kuma, mun samu nasarar kammala aikin shimfida sabon layin dogo mai saurin tafiya na farko a tsakanin biranen Beijing, babban birnin kasar Sin da birnin Tianjin. Wannan sabon layin dogo ya iya wakiltar fasahohin zamani na jiragen kasa da muka mallaka."

Ibrahim: jama'a masu sauraro, tsawon sabon layin dogo mai saurin tafiya na farko da aka shimfida a tsakanin biranen Beijing da Tianjin ya kai kilomita 120. An fara aikin shimfida shi ne a watan Yuli na shekara ta 2005, sannan layin ya fara aiki a ran 1 ga watan Augusta na shekarar 2008. Saurin jiragen kasa dake tafiya a kan wannan sabon layin dogo ya kai kilomita 350 a cikin sa'a daya. Wannan ya alamta cewa, kasar Sin ta kai wani sabon matsayi wajen shimfida sabon layin dogo mai saurin tafiya.

Sanusi: ai, malam Ibrahim, bayan an kaddamar da wannan sabon layin dogo mai saurin tafiya a tsakanin biranen Beijing da Tianjin, sannan a shekara ta 2010, an kaddamar da sabbin layukan dogo masu saurin tafiya a tsakanin biranen Zhenzhou da Xi'an, da kuma a tsakanin biranen Shanghai da Nanjing, sai a tsakanin biranen Shanghai da Hangzhou, sannan kuma a tsakanin biranen Fuzhou da Xiamen da dai sauransu. Bugu da kari, an kaddamar da ayyukan yau da kullum na wani sabon layin dogo mai saurin tafiya a tsakanin biranen Beijing da Shanghai, wato birane biyu mafi muhimmanci a kasar Sin da tsawonsa ya kai kilomita kusan 1300. Lokacin da ake gwajin ingancin sabon jirgin kasa mai saurin tafiya da wannan sabon layin dogo a kan sabon layin dogo tsakanin Beijing da Shanghai, gudun jirgin kasa a kan wannan sabon layin dogo ya kai kilomita 486.1 cikin sa'a daya. Sabo da haka, wannan sabon layin dogo ya zama wata sabuwar alama a duniya wajen yin amfani da fasahohin zamani na layin dogo mai saurin tafiya.

Ibrahim: e, haka ne. a yayin babban taro game da sabon layin dogo mai saurin tafiya karo 7 da aka yi a nan birnin Beijing a karshen shekara ta 2010, Mr. Rubinu, babban direktan kawancen layin dogo ta kasa da kasa ya yaba wa kasar Sin cewa, "Yanzu kasar Sin tana da tsari mafi girma dangane da sabbin layukan dogo masu saurin tafiya, kuma wannan tsari zai ninka har sau 2 ko uku a cikin shekaru 10 ko 20 masu zuwa. Ko shakka babu, kasar Sin za ta kasance a kan gaba a duniya a fagen sabbin layukan dogo masu saurin tafiya."

Sanusi: an labarta cewa, ya zuwa shekara ta 2012, tsawon layukan dogo na kasar Sin zai kai kilomita dubu 110, kuma za a shimfida sabbin layukan dogo masu saurin tafiya guda 4 daga arewa zuwa kudancin kasar, sannan za a shimfida sauran sabbin layukan irin wadannan guda 4 daga gabas zuwa yammacin kasar. Wadannan sabbin layukan dogo masu saurin tafiya za su hade kusan dukkan muhimman birane da yankunan da suka samu ci gaba sosai ta fuskar tattalin arziki.

Ibrahim: a cikin shekaru 5 masu zuwa, kasar Sin za ta kasance tamkar kasar dake shimfida sabbin layukan dogo masu saurin tafiya cikin sauri sosai, kuma ta mallaki kusan dukkan fasahohin zamani na shimfida sabbin layukan dogo masu saurin tafiya, har ma da kera jiragen kasa masu saurin tafiya. Sakamakon haka, wadannan sabbin layukan dogo masu saurin tafiya da jiragen kasa masu saurin tafiya suna canja harkokin zirga-zirga da ake ciki a kasar Sin. Ba ma kawai ana iya tsimin makamashi da kiyaye ingancin muhalli ba lokacin da ake amfani da sabbin jiragen kasa masu saurin tafiya, har ma ana iya bunkasa sauran masana'antun da suke da nasaba da sabbin jiragen kasa da sabbin layukan dogo masu saurin tafiya, har ma sun zama muhimman sana'o'in da za a ci gajiyarsu a nan gaba. Mr. Zhang Dejiang, mataimakin firaministan gwamnatin kasar Sin ya bayyana cewa, "An daga matsayin kasar Sin wajen zamanintar da layukan dogo sakamakon bunkasa sabbin layukan dogo masu saurin tafiya da sabbin jiragen kasa masu saurin tafiya da ta yi. Haka kuma, an kara karfin hukumomin layukan dogo wajen sufurin kayayyaki. Sannan, sun sassauta hali mai tsanani da ake ciki ta fuskar ci gaban tattalin arziki sakamakon rashin isashen karfin sufurin kayayyakin da ake fuskanta a da. Bugu da kari, sabbin layukan dogo masu saurin tafiya sun amfanawa masana'antun kere-kere da nazarin sabbin kayayyakin da ake bukata da kuma bunkasa sana'o'in ba da hidima cikin sauri. Dadin dadawa, ya taka muhimmiyar rawa wajen kyautata tsarin sana'o'i da raguwar yawan gonakin da aka mamaye domin shimfida layukan dogo na yau da kullum da inganta rayuwar jama'a da dai sauransu."

Sanusi: e haka ne, malam Ibrahim, ba ma kawai sabbin layukan dogo masu saurin tafiya suna taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa tattalin arziki ba, har ma jama'a sun samu moriya sosai. Ko su tafi yawo, ko su kai ziyara ga dangogi da abokai ko su je karatu a wasu wurare, hakika sabbin layukan dogo masu saurin tafiya sun canja rayuwarsu.

"sabo da ba wani bata lokaci sosai ba a kan hanya, za mu iya samun isashen lokaci domin yawon bude ido."

"A da, idan za mu je birnin Nanchang, dole ne mu shafe sa'o'i biyu ko fiye a kan hanya. Yara ba su da hakuri, kuma ba su so su zauna a cikin jirgin kasa fiye da sa'o'i biyu. "

"yanzu mun samu sauki sosai sabo da wannan jirgin kasa mai saurin tafiya. Na ga kamar ina wasa a gida, ban yi wata tafiya mai nisa ba."

Ibrahim: Bisa labarin da aka bayar, an ce, a lokacin da ake jin dadin hutun bikin bazara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, sabon layin dogo mai saurin tafiya ya kasance zabi na farko da mutanen da suke zaune a yankunan dake kusa da birnin Shanghai suka yi lokacin da suke yawon bude ido. Lokacin da ake kokarin shimfida sabbin layukan dogo masu saurin tafiya a nan kasar Sin, suna kuma yin tasiri ga zaman rayuwar yau da kullum ta Sinawa. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China