A ran 20 ga wata, gwamnatin kasar Libya ta fara bayar da makamai ga jama'arta, jama'a da dama sun taru a wurin Mouammer al Gaddafi, sun bayyana cewa, za su tabbatar da tsaron kasar da kuma na Gaddafi.
A wannan rana, kungiyar kawancen kasashen Larabawa ta yi tir da hare-haren da kasashen yammacin duniya suka kai wa kasar Libya.
Kana kasar Rasha ta yi kira ga kasashen Amurka da Ingila da Faransa da su dakatar da kai hare-hare ga kasar Libya. Kuma ma'aikatar harkokin waje ta kasar Indiya ta bayar da wata sanarwa, inda ta nuna takaici ga hare-haren da aka kai wa kasar Libya.
A wannan rana, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Iran ya bayyana cewa, kasarsa ta yi Allah wadai da hare-haren da kasashen yammacin duniya suka kai wa kasar Libya.
Amma wasu kasashe sun nuna goyon baya ga kai hare-hare a kasar Libya. Bayan da aka kai hare-haren, kasashen Australia da New Zealand da Italy da Czech da Belgium da kuma Turkiya sun nuna goyon baya ga kasashen Amurka da Ingila da Faransa da suka kai hare-haren.(Zainab)