in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka, Birtaniyya da Faransa sun fara kai hari ga kasar Libya
2011-03-20 13:32:05 cri

A ranar 19 ga wata, kasashen Faransa, Amurka da Birtaniyya da dai wasu kasashen yamma sun fara kai hari ga kasar Libya, yayin da hukumar kasar Libya ta tabbatar da ganin hare-haren makamai masu linzami da ake yi wa wurare daban daban na kasar, haka kuma ta yi Allah wadai da irin harin da kasashen yamma ke kokarin kai wa kasa ta Libya.

Kakofin watsa labaru na kasar Faransa sun bayyana a ranar 19 ga wata cewa, jiragen saman yaki na kasar Faransa sun riga sun kai hare-hare kan kasar Libya har sau 4 a ran nan, inda suka haddasa lalacewar wasu motocin yaki. Labaran da aka bayar sun bayyana cewa, jiragen saman yaki na kasar Faransa fiye da 20 sun shiga hare-haren da aka yi.

A nasa bangaren, Willam E. Gortney, babban darektan hedikwatar ba da nasiha ga rundunar sojan Amurka, ya furta a ranar 19 ga wata cewa, jiragen ruwan yaki na Amurka da Birtaniyya da ke bahar Rum sun harbi makamai masu linzami fiye da dari ga kasar Libiya, wadanda suka haddasa lalacwar sansanonin kin hare-haren da za a kai daga sama fiye da 20 a kasar. An ce, kasashen da suke kokarin kai hare-hare ga Libya sun hada da Amurka, Birtaniyya, Faransa, Kanada, da Italiya.

Haka zalika, ma'aikatar harkokin waje ta kasar Libya ta sanar a ranar 19 ga wata da cewa, kuduri mai lamba 1973 da MDD ta zartas dangane da hana haramcin tashin jiragen sama a Libya ya riga ya rasa amfani, ganin yadda kasar Faransa ta zama wadda ta fara keta kudurin, don haka yanzu Libya tana da ikon kare kanta da jiragen saman yaki nata.

Daga bisani kuma, gidan telabijin kasar Libya ya ba da labarin a ranar 20 ga wata cewa, zuwa yanzu mutanen kasar kimanin 48 sun rasa rayuka sakamakon hare-haren sama, yayin da wasu 150 suka jikkata, wadanda akasarinsu mata,yara da tsoffi ne.

Haka kuma a nasa bangare shugaban kasar Libya Muammar Gaddafi ya yi jawabin ta gidan telabijin kasar a ranar 19 ga wata, wasu sa'o'i bayan da aka kai hare-hare ga kasarsa, inda ya ce yanzu ya dace a samar wa jama'ar kasar da makamai domin su kare 'yancin kan kasa.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China