An labarta cewa, shugabannin kungiyoyin duniya da kasashe da dama ciki har da babban sakataren MDD Ban Ki-moon, da babban sakataren kawancen kasashen Larabawa Amr Mahmoud Moussa, da Herman Van Rompuy, shugaban din din din na kwamitin kula da harkokin kungiyar EU, da Madam Catherine Ashton, babbar wakiliyar kungiyar EU ta fuskar manufofin diplomasiyya da tsaro, da firaminsitan kasar Birtaniya David Cameron, kana da Madam Angela Merkel, shugabar gwamnatin kasar Jamus za su halarci taron, inda za su tattauna kan yadda za a aiwatar da kudurin da kwamitin sulhu na MDD ya zartas a ran 17 ga wata kan halin da kasar Libya ke ciki.(Kande Gao)