in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu na MDD ya tsai da kudurin kafa yankin hana shawagin jiragen sama a kasar Libya
2011-03-18 09:45:15 cri

A ran 17 ga wata, kwamitin sulhu na MDD ya zartas da kudurin kafa yankin hana shawagin jiragen sama a kasar Libya, kana ya bukaci kasashen da abin ya shafa da su dauki matakan tabbatar da tsaron jama'ar kasar da yankunan da suke rayuwa.

A wannan rana da safe, kwamitin sulhu na MDD ya jefa kuri'u kan shirin kudurin da kasashen Faransa da Lebanon da Ingila da kuma Amurka suka gabatar tare. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, kasashe 10 cikin kasashe 15 membobin kwamitin sun amince da wannan kuduri, kasashen Sin da Rasha da Indiya da Jamus da kuma Brazil sun janye daga kada kuri'a.

Kudurin ya ce, don tabbatar da tsaron jama'ar kasar Libya, za a hana shawagin jiragen sama a kasar ban da jiragen sama na jin kai da kuma jigilar mutanen kasashen waje zuwa kasashensu. Kana kudurin ya nuna cewa, ba za a tura sojojin kasa zuwa kasar Libya ba.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China