Sanusi: Kamfanin Envision na Mr. Zhang Lei yana unguwar bunkasa kimiyya da fasaha ta Jiangyin. A cikin wani daki na sashen injiniya na kamfanin, akwai wani babban allo na zamani, inda ake bayyana yadda injunan samar da wutar lantarki masu aiki da makamashin iska da aka kafa su a wurare daban daban na kasar Sin suke aiki. Mr. Xie Dekui, wanda ke kula da wannan sashen ya bayyana cewa, "Wannan daki shi ne cibiyar kamfaninmu ta sa ido kan yadda injunanmu ke aiki a duk fadin duniya. Muna kokarin bayyana kafar da aka yi amfani da ita wajen samar da 'wutar lantarki daga makamashin iska', daga wani wuri, za a iya sarrafa dukkan injunan samar da wutar lantarki masu aiki da makamashin iska da suke aiki a wurare daban daban na duniyarmu, kuma a wannan wuri, za a iya samar da dabarun daidaita matsalolin da wadannan injuna ke fuskanta. Yanzu yawan injunanmu da suke samar da wutar lantarki a wurare daban daban ya kai dari 2, sannan yawansu da aka kafa ya kai dari 1."
Ibrahim: Lallai malam Sanusi, Duk wanda ya samu nasara yana da wani mafari, wato akwai burin da yake son cimmawa. Yau fiye da shekaru 10 da suka gabata, lokacin da Mr. Zhang Lei yake karatu da aiki a ketare, yana da wani buri, wato yana son zayyana wani tsarin samar da wutar lantarki mai aiki da makamashin iska dake dacewa da halin da ake ciki a kasar Sin. A ganinsa, sana'ar yin amfani da makamashin iska domin samar da wutar lantarki tana da kyakkyawar makoma, kuma ya amince da cewa, yin amfani da makamashi maras fitar da abubuwan gurbata muhalli ya zama wajibi ga bil Adam, kuma makamashin iska makamashi ne mai tsabta da yake iya yin takara da makamashin gargajiya, kamar man fetur da kwal da aka dade ake amfani da su.
Sanusi: sai dai malam Ibrahim, a watan Faburairu na shekarar 2007, Mr. Zhang Lei da sauran mutane gomai sun dawo garin Jiangyin dake gabashin kasar Sin, inda suka kafa kamfanin kera injunan samar da wutar lantarki masu aiki da makamashin iska da cibiyar sa ido kan yadda irin wadannan injuna suke aiki a wurare daban daban na kasar Sin. A watan Afrilu na shekarar 2008, sun samu nasarar kera wani sabon injin samar da wutar lantarki mai aiki da makamashin iska da suke da ikon mallakar fasaha. Kuma wannan inji ya soma aiki, kuma ya iya samar da wutar lantarki ga tsarin rarraba wuta. Ya zuwa yanzu, fasahohin irin wannan injin da kamfanin Envision ke samarwa suna kan gaba a duk duniya, kuma yawan wutar lantarki da yake samarwa yana da yawa.
Ibrahim:A cikin kusan shekaru 3 da suka gabata kawai, Mr. Zhang Lei da kungiyarsa sun kammala ayyukan samar da takardun zane-zane da samar da wani samfurin injin samar da wutar lantarki mai aiki da makamashin iska, har ma sun soma samar da wutar lantarki ga tsarin rarraba wuta. Haka kuma yanzu kamfanin Envison ya zama kamfani na farko dake iya zayyana tsarin sarrafa injunan samar da wutar lantarki masu aiki da makamashin iska da karfin kowanensu ya kai fiye da megawatts daya a kasar Sin.
Sanusi: A bara, yawan kudin da aka sayar da irin wadannan injunan da kamfanin Envision ya samu ya kai kudin Sin yuan biliyan 2, kuma Zhang Lei ya kusan cimma burinsa. Kamar yadda Mr. Zhang Lei ya furta cewa, "Fasaha mafi muhimmanci da muke mallaka tana kan gaba a duniya. Musamman a kwanan baya, mun kirkiro wata sabuwar fasahar da ba a taba ganin irinta ba a tarihi, wato tsawon fankar da muke amfani da ita a cikin injinmu ya kai mita 87. Sakamakon haka, yawan wutar lantarki da zai iya samarwa zai karu da kashi 10 cikin kashi dari bisa na injin gargajiya."
Ibrahim: Sabo da shi ne ya kafa, kana ke tafiyar da wannan kamfanin nazari da kera injunan samar da wutar lantarki masu aiki da makamashin iska, Mr. Zhang Lei yana ganin cewa, dole ne ya gayyaci wadanda suka kware sosai kan fasahohin zamani daga wurare daban daban don su yi aiki a kamfaninsa. Wannan ne hanya kadai da ya iya bi domin bunkasa kamfaninsa. Ya zuwa yanzu, yawan mutanen da suka kware sosai kan fasahohin zamani iri iri ya kai fiye da dari 2, kuma yawan mutanen da suke da digiri na biyu ko fiye ya kai kashi 40 cikin kashi dari, sannan matsakaicin yawan shekarun haihuwansu bai wuce shekaru 35 ba. Mr. Xie Dekui ya kara da cewa, "Ko wace rana muna fito da wani sabon burin da muke kokarin cimmawa. Yanzu mun canza wannan kamfanin ya zuwa kamfanin dake samar da fasahohin yin amfani da makamashi mai tsabta."
Sanusi: Ai malam Ibrahim, Kirkiro sabbin fasahohin zamani hanya ce ta kasancewa da kuma ci gaban kowane kamfani a kasuwa. Kungiyar dake karkashin jagorancin Zhang Lei ta kan sa ido kan fasahohin zamani na samar da wutar lantarki mai aiki da makamashin iska. Sabo da haka, tana kan gaba a duk kasar Sin, har ma a duk duniya.
Ibrahim: Mr. Zhang Lei ya ce, kamfaninsa ba wani kamfanin kere-kere ne ba, a'a kamfani ne dake mallakar fasahar zamani, kuma ke alamta darajar ilmi. Yanzu cibiyar kera da ba da hidima ga injunan samar da wutar lantarki masu aiki da makamashin iska tana garin Jiangyin, sannan cibiyar tafiyar da harkokin kasuwanci tana birnin Shanghai, kuma cibiyar kirkiro sabbin fasahohin zamani tana kasar Denmark. Haka kuma, kasar Amurka ta kasance tamkar wata babbar kasuwa ga kamfanin Envision na Mr. Zhang Lei. Mr Zhang ya ce, "a kullum mu kan tambayi kanmu cewa mene ne burin da muke son cimmawa? Muna son zama wani kamfanin dake iya wakiltar dabarun jama'ar kasar Sin dake samun girmamawa daga bangarori daban daban. Sabo da wannan nauyin dake bisa wuyanmu ya sa kamfaninmu ya jawo masana da yawa."
Sanusi: Lokacin da yake bayani kan makomar kamfanin Envision, Mr. Zhang Lei ya ce, zai yi gwaje-gwaje iri iri a cikin kamfaninsa na Envision domin neman wata hanyar yin amfani da makamashi mai tsabta dake dacewa da hakikanin halin da ake ciki a kasar Sin. Sannan za a kafa cibiyar yin gwajin wutar lantarki na iska daidai da matsayin kasar. Bugu da kari, zai kafa hukumar yin nazari da kera sabbin injunan samar da wutar lantarki masu aiki da makamashin iska a ketare. A waje daya, yawan kayayyakin gyara da kamfanin Envision dake garin Jiangyin ya samar zai wuce kashi 50 cikin kashi dari. Mr. Zhang Lei na kokarin yin amfani da shekaru 10 wajen bunkasa kamfaninsa da ya zama wani babban kamfanin dake mallakar fasahohin zamani masu tsabta kuma marasa fitar da abubuwan gurbata muhalli wanda ke kan gaba a duk duniya. (Sanusi Chen)