in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zaman karko na al'ummar kasar Sin sharadin farko ne na bunkasuwar tattalin arziki kasar Sin mai dorewa
2011-03-16 10:27:34 cri

Duk da cewa an kawo karshen manyan taruruka biyu yadda ya kamata, kafofin yada labaru na kasashen ketare da Sinawa dake kasashen waje sun ci gaba da mai da hankali kan taruruka, kuma sun bayyana cewa, zaman karko na al'ummar kasar Sin sharadin farko ne na bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin mai dorewa. Ta hanyar kafofin yada labaru na Sinanci a ketare, wasu Sinawa sun yi kira da a kara kokarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.

Kafar yada labaru ta nahiyar Latin Amurka ta ba da labari cewa, Sin ta shiga wani sabon mataki na fuskantar sabbin kalubaloli, kamata ya yi, Sin ta magance wadannan kalubaloli domin tabbatar da zaman karko mai dorewa.

Jaridar Safe ta kasar Singapore ta ba da sharhi mai take "Tabbatar da zaman karko tare da samun bunkasuwa" cewa, yanzu kasar Sin ta kasance wata kasa dake kawo babban alhanu ga duniya. A cikin shekaru biyar masu zuwa, Sin za ta samu bunkasuwa yadda ya kamata, wannan ba ma kawai zai yi amfani ga kasar Sin, har ma zai kawo alhanu mai kyau ga duniya.

Babban direktan jaridar European Times ta kasar Faransa Zhang Xiaobei ya ce, tsarin shekaru biyar a karo na 12 na kasar Sin ya jaddada wajibcin samar da adalci cikin al'umma, wannan zai kawo zarafi mai kyau ga ci gaban al'ummar kasar Sin tare da ba da taimako ga tabbatar da zaman karko a kasar Sin.(Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China