in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ofishin hukumar kwastam mafi kankanta na goyon bayan kasuwar cinikin kananan kayayyaki mafi girma a kasar Sin
2011-03-14 18:10:36 cri
Ibrahim: Ofishin hukumar kwastam, shi kadai da aka kafa a gundumar Yiwu ta lardin Zhejiang shi ne ofishi mafi kankanta a kasar Sin, amma yana da nasaba da bunkasuwar kasuwar Yiwu ta fuskar cinikin kananan kayayyaki mafi girma a duniya.

Sanusi: An kafa wannan ofishi na hukumar kwastam a gundumar Yiwu ne a shekarar 2009. Ko da yake gundumar Yiwu karama ce, amma sabo da kasuwar Yiwu ta yi suna sosai, yawan kayayyakin da ake shigarwa da fitarwa a wannan kasuwa yana da yawa. Mr. Zhang Jun, shugaban ofishin hukumar kwastam ta Yiwu ya bayyana cewa, "Bisa kididdigar da aka yi, an ce, yawan kananan kayayyakin da aka fitar daga kasuwar Yiwu zuwa kasashen waje ya kai akwatuna dubu 519 a shekarar 2009, sannan wannan adadi ya kai dubu 576 a shekarar 2010. Bugu da kari, kafin a kafa ofishin hukumar kwastam a Yiwu, yawan harajin da kamfanonin wurin suka biya bai wuce kudin Sin yuan miliyan 10 ba, amma bayan kafuwar ofishin a shekarar 2009, yawan harajin da suka biya ya kai kudin Sin yuan miliyan 183 a shekarar 2010."

Ibrahim: sai dai malam Sanusi, sabo da ba a iya fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje kai tsaye ta filin jirgin sama na Yiwu, bayan kafa ofishin hukumar kwastam ta Yiwu, sai aka fara daidaita harkokin ofishin hukuma ta kwastam a Yiwu, sannan an yi amfani da motocin daukar kaya wajen sufurin kayayyaki zuwa filin jirgin sama na Pudong dake birnin Shanghai domin fitar da su zuwa kasashen waje. Sakamakon haka, aka saukaka ajandar fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje a garin Yiwu. An kafa kamfanin sufurin kayayyaki na Yangxiang, wato kamfanin da ya fara wannan aiki a shekarar 2001. Madam Jin Lixian, wadda ke kula da wannan kamfani ta bayyana cewa, "Bayan kafa ofishin hukumar kwastam a garin Yiwu, yawan kayayyakin da kamfaninmu ke sufuri ya karu da kimanin kashi 30 cikin dari. A shekarar 2008, kamfaninmu da kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na China Eastern mun taba tattaunawa kan yadda za mu hada gwiwa a tsakaninmu ta fuskar sufurin kayayyakin da ake fitarwa. Kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na China Eastern ma yana son samun kwangilolin sufurin kayayyaki a garin Yiwu. Amma sabo da wasu dalilai, ba mu samu nasara ba. Bayan kafuwar ofishin hukumar kwastam a garin Yiwu, mun cimma matsayi daya wajen hada kamfaninmu da jiragen sama na kasa da kasa a tsakanin kamfanonin daukar kaya da kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama na daukar kaya. Alal misali, a da, idan 'yan kasuwa sun kawo mana kayayyakinsu a yau, sai gobe mu gabatar da wadannan kayayyaki ga ofishin hukumar kwastam ta Shanghai, sannan a jibi ne za a iya sufurinsu zuwa kasashen waje, wato ana bukatar kwanaki uku domin a kammala matakan da suka dace. Amma yanzu, idan dan kasuwa ya kawo mana kayayyakinsu kafin karfe 8 na safe, za mu iya kammala ayyukan neman izinin fitar da su zuwa kasashen waje a ofishin hukumar kwastam ta Yiwu kafin karfe 11 da rabi na safe, sannan jiragen dakon kaya za su iya yin sufurin kayayyaki zuwa kasashen waje kafin karfe 12 na dare. Ofishin hukumar kwastam na Yiwu ya taka muhimmiyar rawa sosai ga sufurin kayayyaki da kasuwar kananan kayayyaki na Yiwu."

Sanusi: Mr. Leo, wan dan kasuwa ne da ya zo kasar Sin a sheakrar 2006 daga kasar Columbiya. Yanzu yana tafiyar da wani kamfanin shige da ficen kayayyaki a garin Yiwu. Ya gaya wa wakilinmu da harshen Spaniya cewa, "A lokacin da na zo nan kasar Sin, akwai sarkakiya sosai wajen daidaita harkokin fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje. Alal misali, a kan shafe wasu kwanaki domin yin hayar akwatunan daukar kaya, sannan mun je hukumar kwastam da kuma tabbatar da motocin daukar kayan. Mu kan shafe mako daya ko makonni biyu domin lodin kayayyakinmu a jiragen ruwa. Amma yanzu, mun kan shafe kwanaki 2 ko hudu ne kawai mu kammala wadannan ayyuka."

Ibrahim: bugu da kari, bayan da ofishin hukumar kwastam na Yiwu ya mai da hankali sosai wajen kare ikon mallakar fasaha a kokarin kiyaye sunan kasuwar kananan kayayyaki ta Yiwu a duniya domin tabbatar da ganin kasuwar ta samu ci gaba kamar yadda ya kamata. Mr. Zhang Jun ya kara da cewa, "A shekarar 2010, ofishin hukumar kwastam na Yiwu ya yi bincike kan matsalolin satar ikon mallakar fasaha 449, wato ta kiyaye halaltaccen ikon mallakar fasaha da yawansu ya kai fiye da dari 2 da suke da nasaba da kasashe fiye da 20."

Sanusi: haka kuma, ofishin hukumar kwastam na Yiwu ya kafa wani dakin nune-nunen ilmin kare ikon mallakar fasaha. A cikin wannan daki, ana iya ganin matsalolin da suka shafi satar ikon mallakar fasaha da hukumar ta bincika a cikin 'yan shekarun nan, ana kuma iya ganin lambobin yabo da wasu manyan kamfanonin kasashen duniya suka bai wa hukumar. Sannan, hukumar ta kan gayyaci 'yan kasuwa na kasashen waje da na cikin gida wadanda suke aiki a kasuwa da su kai ziyara wannan daki domin samun ilmin kare ikon mallakar fasaha da kuma moriyarsu ta halal. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China