A gun taron manema labaru bayan taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, Wen Jiabao ya bayyana cewa, kamata ya yi a yi kwaskwarima kan tsarin siyasa tare da tsarin tattalin arziki bisa daidaici, kwaskwarimar da ake yiwa tsarin siyasa tabbaci ne ga tsarin kwaskwarima kan tsarin tattalin arziki. A halin yanzu, babbar matsalar da kasar take fuskanta ita ce cin hanci, ana bukatar yin kwaskwarima kan tsarin mulki da tsarin hukumomi ta hanyar yaki da cin hanci. Kana ya ce, adalci halayen musamman ne na gurguzu, wanda ke tabbatar da zaman lafiyar al'ummar kasar. Ba ma kawai kasar Sin tana bukatar cimma burin rarraba albashi cikin adalci, hatta ma tana bukatar rarraba albarkatu a fannonin ba da ilmi da kiwon lafiya da sauransu cikin adalci.(Zainab)