in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a fi dora muhimmanci kan daidaita hauhawar farashin kayayyaki a kasar Sin a bana, in ji firaminista Wen Jiabao
2011-03-14 14:38:25 cri

A ran 14 ga wata, a birnin Beijing na Sin, firaminista Wen Jiabao ya bayyana cewa, a bana za a dauki matakan kyautata hauhawar farashin kayayyaki a matsayi na farko na aikin kyautata harkokin kasar daga manyan fannoni da gwamnatin Sin za ta yi. Sin tana da kwarin gwiwa wajen shawo kan kiyasin hauhawar farashin kayayyaki.

Wen ya ce, yanzu ana fama da hauhawar farashin kayayyaki a kasar Sin. Dalilin da ya sa haka shi ne wasu kasashe suna gudanar da manufar kudi mai sassauci. Hakan ya yi sanadiyyar tangal-tangal ga sauyin kudi da na farashin kayayyaki mai tsanani. Bayan haka, a cikin kasar Sin kuma, ana fuskantar hauhawar farashin kayayyaki a sakamakon hauhawar darajar lebura da dai sauransu.

Bayan haka, Wen ya bayyana cewa, Sin za ta shawo kan kiyasin hauhawar farashin kayayyaki daga fannoni uku, wato na farko, kara bunkasa aikin samarwa, musamman ma aikin gona domin samar da isashen abinci. Na biyu, kara karfin yin sufuri, musamman ma yin jigilar amfanin gona. Na uku, ba da kulawa ga kasuwanni ta hanyar amfani da tsarin tattalin arziki da dokoki.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China