A cikin shirin raya zaman al'umma da bunkasa tattalin arziki cikin shekaru 5 masu zuwa, Sin ta yi shirin raya tattalin arziki da saurin karuwarsa ya kai kashi 7 cikin 100, kuma idan aka kwatanta wannan adadi da na shirin shekaru biyar-biyar da ya gabata, akwai bambanci da kashi 0.5 cikin 100.
Mr. Wen ya ce, dole ne kasar Sin ta daidaita matsalolin da ke kasancewa tsakanin saurin karuwar tattalin arziki da samar da guraben aikin yi da matsalar hauhawar farashin kayayyaki, kuma Sin za ta kyautata salon raya tattalin arziki wajen warware matsalar rashin raya tattalin arzikin cikin daidaici da ke kasancewa har na wani tsawon lokaci da rashin samun bunkasuwa cikin dogon lokaci, don raya tattalin arziki da ya dace da raya al'umma da kiyaye muhalli da raya makamashi, yayin da aka tabo maganar samar da guraben aikin yi, Mr. Wen ya ce, za a raya masana'antu na kanana da matsakaita, da kara raya sana'ar yin hidima don kara samar da guraben aikin yi.(Bako)