in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ba a iya kwatanta kasar Sin da kasashen yammacin nahiyar Asiya da na arewancin nahiyar Afirka da suka samu tashe-tashen hankali ba
2011-03-14 12:51:56 cri

A ran 14 ga wata, firaministan kasar Sin Wen Jiabao ya bayyana cewa, ba a iya kwatanta kasar Sin da kasashen yammacin nahiyar Asiya da na arewancin nahiyar Afirka da suka samu tashe-tashen hankali ba.

Wen Jiabao ya jaddada cewa, kasar Sin tana kokarin yin kwaskwarima da raya kasa, kana ba ta fatan a mai da hanyar raya kasar a matsayin wani misalin samun bunkasuwa ba. A ganin kasar Sin,kamata ya yi kasa da kasa su bi hanyar raya kasa da ta dace da halinsu, kuma kasar Sin ta girmama hanyoyin da jama'ar kasa da kasa suka zaba. Kana ana iya girmama da koyi fasahohi da juna kan hanyoyin raya kasa irin daban daban.

Wen Jiabao ya ce, kasar Sin ta bi wata hanyar raya kasa dake dace da halin da ake ciki a kasar. A shekaru fiye da 30 bayan da aka bude kofa da yin kwaskwarima a kasar, tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar Sin sun samu bunkasuwa cikin sauri, kana an kyautata zaman rayuwar jama'a, amma duk da haka, kasar Sin wata kasa ce mai tasowa. Hanyar raya kasar ita ce tsaya tsayin daka kan manufar raya tattalin arziki, da yin la'akari da jama'a, da kuma tabbatar da adalci da kuma ikon demokuradiyya na jama'ar kasar.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China