in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a birnin Beijing
2011-03-14 10:17:01 cri

A ran 14 ga wata da safe, bayan kammala dukkan ayyukan da aka tsara, an rufe taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a birnin Beijing. Shugabannin kasar Sin, kamar Hu Jintao, Wu Bangguo, Jia Qinglin da dai sauransu, sun halarci wannan taro, inda shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Wu Bangguo ya ba da jagoranci.

A gun wannan taro, an zartas da rahoton aikin gwamnatin kasar da firaminista Wen Jiabao ya yi, da zartas da shirin shekaru biyar a karo na 12 wajen bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar Sin, da zartas da shirin bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al'umma na shekarar 2011 da rahoto kan kasafin kudi na shekarar 2011, da zartas da rahoton aikin zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da na kotun koli da na babbar hukumar gabatar da kararraki.

A gun bikin rufe taron, Wu Bangguo ya yi jawabin cewa, a kan wannan sabon mataki, kamata ya yi mu karfafa da kyautata aikin kafa dokoki, da sa kaimi ga kafa dokoki bisa kimiyya da fasaha da demokuradiyya, da ci gaba da kyautata tsarin dokoki na gurguzu mai alamar kasar Sin. Kuma kamata ya yi mu kara mai da hankali kan amfani da dokoki, domin kiyaye kwar-jini da mutumtaka na kundin tsarin mulki da ta dokokin kasar, da sa kaimi ga gudanar da ayyuka bisa dokoki da kokarin samun adalci a fannin yanke shari'a, da karfafa ra'ayin jama'a na tsarin dokoki, ta yadda za a gudanar da tsarin aiwatar da harkokin kasa bisa dokoki a kowane fanni, da kokarin kafa wata kasar gurguzu mai dokokin da suka dace da jama'a.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China