in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe taron shekara-shekara karo na 4 na CPPCC
2011-03-13 16:21:36 cri

An rufe taron shekara-shekara karo na 4 na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin wato CPPCC ta 11 a ranar 13 ga wata a nan birnin Beijing.

A yayin bikin rufe taron da aka shirya a wannan rana, an zartas da kudurin da taron ya gabatar game da ayyukan da zaunannen kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar ya yi, da kuma zartas da rahoton da kwamitin kula da shirin kuduri na majalisar ya bayar game da yadda aka dudduba shirin kuduri a gun taron, gami da zartas da kudurin siyasa na wannan taro.

Shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin, Jia Qinglin ya yi jawabi a yayin bikin rufe taron cewa, an samu cikakkiyar nasara wajen kawo karshen ajandar taron. A lokacin taron, 'yan majalisar sun ba da shawarwari masu muhimmanci kan batutuwan dake da nasaba da gaggauta canza hanyar raya tattalin arziki, da kyautata tsarin tattalin arziki, da ba da tabbaci da kyautata zaman rayuwar jama'a, da bunkasa al'adu irin na raya gurguzu, da karfafa aikin kula da zamantakewar al'umma, da tabbatar da samun zaman karko da wadatuwa a yankunan musamman na Hongkong da Macau, da kuma inganta bunkasuwar dangantakar dake tsakanin gabobin biyu na mashigin tekun Taiwan cikin lumana, wadanda suka nuna muhimmiyar rawa da majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin ke takawa wajen raya kasar. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China